Iran ta kashe sojojin Amurka biyu a Jordan

CENTCOM ta bayyana cewa ba za ta bayyana sunayen sojojin da suka mutu ba har sai an sanar da iyalansu

Iran ta kashe sojojin Amurka biyu a Jordan

Donald Trump

Wasu hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai sun yi sanadin mutuwar sojojin Amurka biyu da kuma ɓacewar wani soja guda a Jordan.

Hedikwatar Tsaron Amurka (CENTCOM) ta tabbatar a shafinta na X cewa lamarin ya faru ne ranar 17 ga Yuli, lokacin da dakarun Amurka da na Jordan ke ƙoƙarin daƙile hare-haren Iran.

CENTCOM ta ce an garzaya da wasu sojojin Amurka huɗu asibitoci a Jordan domin jinya, amma daga bisani aka sallame su bayan an tabbatar da cewa raunukan da suka samu ba su da tsanani, kuma sun koma bakin aiki.

Ta ƙara da cewa ba za ta bayyana sunayen sojojin da suka mutu ba har sai an sanar da iyalansu.

“Saboda girmamawa ga iyalan [waɗanda lamarin ya shafa], CENTCOM za ta riƙe ƙarin bayani, ciki har da sunayen gwarzayen da suka rasu, har zuwa bayan sa’o’i 24 bayan an sanar da ‘yan ‘yanuwansu,” in ji hedikwatar tsaron.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana mutuwar sojojin a matsayin abin takaici, yana mai cewa sun sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa ƙasarsu hidima.

A martaninsa, Trump ya ba da umarnin ƙaddamar da sabbin hare-haren sama kan Iran.

CENTCOM ta ce ta soma cika wannan umarni da yammacin Asabar, kuma manufarsu ita ce ƙara raunana ƙarfin Iran na kai hari kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz, tare da mayar da martani kan harin da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran IRGC ta kai kan sojojin Amurka a Jordan.