Iran ta lashi takobin daukar fansa kan tagwayen hare-haren Kerman
Khamenei, ya lashi takobin daukar fansa mai tsanani kan harin da kasarsa ke zargin Amurka da Isra’ila sun kashe mata mutane 84
Jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya yi alkwarin daukar fansa mai tsanani kan tagwayen hare-haren da suka kashe mutane 84 a kasar.
A ranar Alhamis ministan harkokin cikin gidan Iran, Ahmad Vahidia, ya rage adadin wadanda suka rasu a harin zuwa 84. Da farko hukumomin sun ce adadin ya kai 103.
Shguaban hukumar agajin gaggawar Iran, Jafar Miadfar, ya ce da farko an kirga wasu gawarwaki sama da sau daya, saboda tarwatsewar da suka yi, kafin daga baya a gano hakan.
Miadfar ya ce wadansu mutum 284 sun samu raunuka, inda 195 daga cikinsu ke wance a asibiti a sakamakon harin na Kudancin birnin Kerman.
Khamenei ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Khamenei ya fitar bayan harin a ranar Labara.
Jagoran addinin ya ce “Muggan makiyan al’ummar Iran sun sake haddasa wani bala’i tare da kisan gilla ga al’ummar Kerman.”
Babban mai ba wa shugaban kasar Iran shawara, Mohammad Jamshidi ya zargi Isra’ila da Amurka da hannu a tagwayen hare-haren da suka kashe akalla mutane a Kudancin kasar.“Anna gwamnatin Amurka ta ce ita da Isra’ila ba su da hannu harin na yankin Kerman, Iran. Amma da gaske suke?,” in ji shi a shafinsa na X.