Iran ta nemi mu yi wata ganawar a Qatar — Trump

Za a yi ganawar ce bayan da ƙasashen biyu suka sake kai wa junansu hare-hare a kwanakin nan.

Iran ta nemi mu yi wata ganawar a Qatar — Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Iran ta nemi a gudanar da wata ganawa tsakanin ɓangarorin biyu, wadda za a yi a birnin Doha na ƙasar Qatar a ranar Talata.

Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa, “Iran ta nemi a yi ganawa. Za a gudanar da ita gobe [Talata] a Doha,” sai dai bai bayyana waɗanda za su halarta ba.

Sanarwar ta zo ne duk da cewa Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya musanta rahotannin da ke cewa an shirya tattaunawar tsakanin ƙasashen biyu a wannan makon, inda ya ce har yanzu ba a kammala shiri kan ranar da wurin ganawar ba, kuma masu shiga tsakani na ci gaba da shawarwari kan yadda tattaunawar za ta kasance.

Sai dai kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, ta tabbatar cewa wakilin Amurka, Steve Witkoff, da mashawarcin Trump, Jared Kushner, za su tafi Doha domin halartar tattaunawar  a wannan makon, inda kuma Trump ke fatan ganin an ci gaba da aiwatar da sulhun ba tare da tangarɗa ba.

Wani jami’in diflomasiyya da ke da masaniya kan tattaunawar ya kuma tabbatar da cewa jami’an Amurka da Iran za su gana a Doha domin tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da ɓangarorin suka cimma a farkon wannan watan.

Rahotanni sun ce an samar da hanyoyin sadarwa tsakanin ɓangarorin domin dakile duk wata sabuwar hatsaniya bayan hare-haren baya-bayan nan da suka kai wa juna.

A gefe guda, Iran da Oman sun gudanar da ganawarsu ta farko tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita rikici, inda suka tattauna kan yadda za a tafiyar da mashigin ruwan Hormuz.

Mashigar Hormuz dai na daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, kuma rikicin baya-bayan nan ya haifar da tsaiko ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

Iran ta ce tana ci gaba da sanya ido kan zirga-zirga a mashigar, tare da gargaɗin cewa duk wani yunƙurin kauce wa tsarin da ta shimfiɗa zai iya ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.