Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz har sai abin da hali ya yi

Amurka ta bai wa Tehran wa’adin zuwa jiya Asabar ta dakatar da hare-hare sannan ta buɗe Mashigar Hormuz.

Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz har sai abin da hali ya yi

Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz har sai abin da hali ya yi, bayan sabunta musayar hare-hare tsakaninta da Amurka, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin duniya kan makomar zirga-zirgar jiragen ruwa a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai da iskar gas.

Lamarin ya biyo bayan hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kan wasu wuraren soji a Iran, bayan da dakarun Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran IRGC suka kai farmaki kan wani jirgin ruwan dakon kaya a ranar Asabar.

Jerin hare-haren da ɓangarorin biyu suka yi cikin ’yan kwanakin nan ya sa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma domin kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara a ranar 28 ga watan Fabrairu. Sai dai Trump ya bayyana cewa har yanzu ƙofar tattaunawa tana nan a buɗe.

Iran ta sanar da rufe Mashigar Hormuz ne bayan da ta ce harbin gargaɗin da ta yi ya sami wani jirgin ruwan dakon kaya da ya yi amfani da hanyar da ba ta amince da ita ba.

Tehran ta bayyana cewa jirgin ya yi watsi da umarnin da aka ba shi na bin hanyar da aka amince da ita, inda ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsauri ga duk wani hari ko ƙetare dokokin da ta shimfiɗa a mashigar.

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta Islamic Republic of Iran Broadcasting ta fitar, ta ambato rundunar sojin ruwa ta IRGC tana cewa duk wani katsalandan daga ƙasashen waje ko kuma yunƙurin samar da “haramtacciyar hanya” a mashigar ruwan zai gamu da martani mai muni.

Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa Amurka ta bai wa Tehran wa’adin zuwa jiya Asabar ta dakatar da hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa masu amfani da Mashigar Hormuz, tare da sanar da buɗe mashigar a hukumance.

Sai dai babban abin da ke hana cimma yarjejeniya ta ƙarshe shi ne saɓanin da ke tsakanin ɓangarorin kan yadda za a gudanar da zirga-zirga ta Mashigar Hormuz.

Iran ta dage cewa ita ce za ta ci gaba da kula da zirga-zirgar jiragen ruwa da ke amfani da mashigar, yayin da Amurka ke buƙatar a ba da damar zirga-zirga ba tare da wani cikas ko kuma biyan harajin amfani da hanyar ba.