Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda rikicin Isra’ila da Lebanon

Iran ta sake gindaya wasu sabbin sharuɗa kan rikicin Isra’ila da Lebanon.

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda rikicin Isra’ila da Lebanon

Iran ta sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz, inda ta bayyana cewa har yanzu ba a cika sharuɗan yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka ba.

A cikin wata sanarwa, rundunar IRGC ta ce mashigar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Isra’ila ta janye dakarunta daga Kudancin Lebanon.

Hakazalika ta ce sai an cire katangar jiragen ruwa gaba ɗaya, sannan sojojin Amurka sun fice daga yankin Tekun Fasha.

IRGC ta zargi Amurka da kasa aiwatar da wasu muhimman sassan yarjejeniyar da Shugaban Amurka, Donald Trump, da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, suka rattaba hannu a farkon wannan mako.

Rundunar ta kuma gargaɗi jiragen ruwa da su guji amfani da mashigar, tana mai cewa duk jirgin da ya yi kunnen uwar shegu zai iya fuskantar hatsari.

Matakin na zuwa ne bayan ɗage tattaunawar nukiliyar da aka shirya yi tsakanin Amurka da Iran.

Hakan ya ƙara dagula yanayin rikici tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon.

Ko da yake rundunar sojin Amurka ta sanar da ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa tashoshin jiragen ruwan Iran na tsawon watanni biyu.

Iran ta ce har yanzu ba a cire takunkumin gaba ɗaya ba.

Masana na ganin saɓani kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar na daga cikin abubuwan da suka haddasa wannan rikici.

A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Isra’ila da Hezbollah na ƙoƙarin tsagaita wuta, amma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce dakarun ƙasarsa za su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a Kudancin Lebanon.

Iran ta kuma kafa sabbin dokoki da suka wajabta wa jiragen ruwa samun izini kafin bi ta mashigar Hormuz.

Wannan mataki ya janyo damuwa a duniya saboda muhimmancin mashigar wajen jigilar man fetur a kasuwancin duniya.