Iran ta ‘samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53’

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya ce kasarsa ta sake samun wata rijiyar mai wadda za ta kara wa kasar yawan manta da kashi daya bisa uku na yawan man da take hakowa. Rijiyar man wadda take Kudu maso Yammacin Lardin Khuzestan na da girman da ya kai mil 926, kuma mahukuntan Iran sun ce tana […]

Iran ta ‘samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53’

Hassan Rauhani, Shugaban Qasar Iran

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya ce kasarsa ta sake samun wata rijiyar mai wadda za ta kara wa kasar yawan manta da kashi daya bisa uku na yawan man da take hakowa.

Rijiyar man wadda take Kudu maso Yammacin Lardin Khuzestan na da girman da ya kai mil 926, kuma mahukuntan Iran sun ce tana kunshe da gangar danyen mai biliyan 53.

Iran dai ta dade tana fama da yadda za ta sayar da manta a kasuwar duniya sakamakon tsauraran jerin takunkumin da Amurka ta kakaba mata. Hakan na nufin kudin shigar kasar a fannin sayar da mai zai karu da Dala biliyan 32 idan aka fara hakar man koda kuwa da kashi daya ne, inji Rouhani. Rijiyar man ka iya zama mafi girma ta biyu a kasar Iran, bayan wadda ke da gangar mai biliyan 65 a Ahbaz, inji Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Iran dai ita ce kasa ta hudu a duniya wajen yawan mai, sannan ta biyu a yawan iskar gas.