Iran ta shirya yaki da Amurka da Isra’ila – Shugaban rundunar sojan Iran
Shugaban rundunar sojojin Iran, Janar Hassan Firouzabadi ya gargadi magabtan kasarsa, cewa a shirye suke su fafata yaki da Amurka da Isra’ila, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya ruwaito.“a shirye muke mu fafata yaki da Amurka da Gwamnatin Sahayoniya ta Isra’ila,” kamar yadda aka ruwaito daga bakin Firouzabadi.Ya kuma gargadi kasashen da ke […]
Shugaban rundunar sojojin Iran, Janar Hassan Firouzabadi ya gargadi magabtan kasarsa, cewa a shirye suke su fafata yaki da Amurka da Isra’ila, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya ruwaito.
“a shirye muke mu fafata yaki da Amurka da Gwamnatin Sahayoniya ta Isra’ila,” kamar yadda aka ruwaito daga bakin Firouzabadi.
Ya kuma gargadi kasashen da ke makwaftaka da kasarsa da ke da su bari a yi amfani da kasarsu wajen kai wa Iran hari. “Ba mu da wani mummunan nufin tashin hankali a kasashen da ke yankinmu, amma idan aka yi amfani da sansanin Am,urka da ke yankin wajen kai mana hari, mu mu ma za mu mayar da martani,” inji shi.
kasadr amurka tana da sansanoni da dama a yankin, wadand asuka hada da Bahrain da JKuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Turkiyya.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry ya yi gargadin cewa idan tattaunawar difulomasiyya ta ci ura, to za a yi amfani da karfin soja a kan Iran. Kuma Amurka za yi abin da duk za ta iya.
Firouzabad ya zrgi Amurka da yaudara da barazana. “Shekara 10 da ta wuce, sun zo da rundunarsu, amma da suka fahimci ba za su iya kai mana hari ba, su suka yi gaba,” a cewarsa, da yake watsi da barazanar kai farmakin soja da Amurka ta yi, al’amarin da ya bayyana a matsayin “yaudarar siyasa.”
Shugaba Hasan Rouhani ya bayyana cewa kasashen Turai su daina ruduwa da son kai wa Iran harin soja. kasar Iran dai za ta ci gaba tattaunakwa da kasashejn turai da Amurka, wadanda suka hada da Birtaniya da Faransa da Amurka da Rasha da china da Jamus, don aiwatar da wata yarjejeniya kan shirin nukiliyarta.