Iran ta yanke hukuncin kisa ga wanda ake zargin jami’in CIA ne

Iran ta ce babbar kotun kasar ta yanke hukuncin kisa kan wani dan kasar da aka zarga da yi wa Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA), leken asiri A cikin Iran. An samu Amir Rahimpour da laifin tura bayanan asiri kan shirin nukiliyar kasar ga Hukumar CIA. Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Iran, Gholamhossein Esmaili, ya […]

Iran ta yanke hukuncin kisa ga wanda ake zargin jami’in CIA ne

Iran ta ce babbar kotun kasar ta yanke hukuncin kisa kan wani dan kasar da aka zarga da yi wa Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA), leken asiri A cikin Iran. An samu Amir Rahimpour da laifin tura bayanan asiri kan shirin nukiliyar kasar ga Hukumar CIA.

Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Iran, Gholamhossein Esmaili, ya ce za a zartar da hukuncin kan mutumin “nan ba da jimawa ba.”

“Amir Rahimpour, wanda ma’aikacin leken asiri na CIA ne, kuma ake biyan sa makudan kudade ya yi yunkurin aika muhimman bayanan asiri game da shirin nukiliyar Iran ne ga hukumar leken asirin ta Amurka, kuma an gurfanar da shi gaban shari’a kuma an yanke masa hukuncin kisa, wanda kwanan nan Kotun Koli ta tabbatar da hukunci, kuma nan ba da jimawa ba za a aiwatar da hukuncin a kansa,” Kamfanin Dillancin Labarai na Iran Fars ya ruwaito Esmaili yana fada.

Wadansu mutum biyu da ake zargin ’yan leken asiri ne, an yanke musu hukuncin daurin shekara 15 kowannensu. Sai dai babu karin haske kan ko ’yan wace kasa ce. Sai dai Esmaili ya ce ma’aikatan agaji ne.

Mutum na karshe da aka zartar masa da hukuncin kisa bisa zargin yi wa Amurka leken asiri a Iran shi ne Shahram Amiri, wanda aka rataye a shekarar 2016. Amiri ya kaura zuwa Amurka a daidai ganiyar da hukumomin Washington suka himmatu wajen taka birki ga shirin nukiliyar Tehran. Lokacin da ya koma Iran a shekarar 2010, ya samu kyakkyawar tarba daga ’yan siyasa kuma ya shahara sosai a shirye-shiryen talebijin. Ba a jima ba sai ya bace bat, kafin daga bisani a tabbatar ya fuskanci shari’a kuma an kashe shi sakamakon aikin leken asiri.

Ko a bazarar da ta wuce, Iran  ta yi ikirarin bankado wani gungun ’yan leken asiri su 17, tare da yanke wa wadansu daga cikinsu hukuncin kisa. Sai dai ba a tabbatar ko an zartar da hukuncin kansu ko a’a, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP da Reuters suka ruwaito