Iran ta zargi Ukraine da kai hari kan jirgin ruwanta a Tekun Caspian

Iran ta ce harin ya yi sanadin mutuwar wani ma’aikacin jirgin ruwa guda, yayin da wani ya samu raunuka.

Iran ta zargi Ukraine da kai hari kan jirgin ruwanta a Tekun Caspian

Ƙasar Iran ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda Ukraine ta kai wa wani jirgin ruwanta hari a Tekun Caspian.

A cewar hukumomin Iran, harin ya yi sanadin mutuwar wani ma’aikacin jirgin ruwa guda, yayin da wani ya samu raunuka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce ta miƙa wa jami’an Ukraine takardar ƙorafi kan lamarin, tana mai bayyana harin a matsayin abin da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Sai dai har zuwa lokacin fitar wannan rahoto, Ukraine ba ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar ko ta musanta zargin da Iran ta yi.