Irin matan da ba zan aura ba
“Dan Ubanka ni za ka yi wa iskanci da rainin wayo” Wannan shi ne martanin da wani bawan Allah ya mayar wa abokinsa, lokacin da abokin ya sanar da shi cewa yana so ya nemi kanwarsa da aure. Ni ma na taba jin abokina a lokacin da na kai ziyara gidansu, yana cewa “Wallahi bai […]
“Dan Ubanka ni za ka yi wa iskanci da rainin wayo” Wannan shi ne martanin da wani bawan Allah ya mayar wa abokinsa, lokacin da abokin ya sanar da shi cewa yana so ya nemi kanwarsa da aure.
Ni ma na taba jin abokina a lokacin da na kai ziyara gidansu, yana cewa “Wallahi bai samu mace ta kwarai ba, sai da ya gama iskancinsa a Abuja, sai yanzu y ace ta kwarai yake nema kuma hafiza?” wannan ya fade shi ne bayan innarsa ta sanar da shi bukatar wansa na neman aure a Islamiyyar unguwarsu. To, tambaya ita ce; meke kawo ire-iren wadannan martani?
Ana so mutum, musamman Musulmi ya gina rayuwarsa bisa tsafta da tarbiyya da kuma al’adarsa matukar al’adar bai ci karo da koyarwar addini ba. Sai dai, kash wasu kan dauki rayuwa yadda ta yi musu dadi ko da kuwa gudanar da ita ta saba wa tsarin da al’umma ke tafiya akai. Daga baya kuma sai ka ga mutum, bayan lokaci ya kure masa, ya dawo yana ‘yan kame-kame. Yana kokarin gyara. To, yin gyara kam yana da wahala, domin Bahaushe na cewa “Ba a yin bari, a kwashe duka”
A iya nazari da tuntuba da na yi bisa kan wannan mas’alar, na sami fahimta da dama kuma ina so in yi amfani da wannan hanyar don in fadakar da ‘yan-uwa, musamman iyaye wadanda idanunsu kan rufe lokacin da suka zo aurar da ’ya’yansu mata da kar su manta cewa Allah (S.W.T) zai yi musu hisabi tsakaninsu da ’ya’yansu a gobe kiyama. Ido, sau da yawa, yakan dode yayin da mutum zai aurar da diyarsa. Ba a tantancewa da gudanar da cikakken bincike kan manemin, musamman in hannunsa da shuni, sai kadan daga cikin wadanda Allah ya tarfa wa garinsu nono ke yi.
A kwanakin baya na halarci daura auren wata yarinya a Sakkwato, bayan an daura sai na ji wasu na yin tsegumi, suna cewa “WALLA AN CI AMANAR dIYAG DA” sai na kasa hakuri, na tambaye su dalilinsu, sai wani ya ce da ni “MALLAM, WALLAHI MUJINTA BA NA kWARAI NA BA, DON KA GANNI KO, TO GIDA GUDA MUKA KWANA, KUMA YADDA YAKA ZINA DA dIYAN MUTANE BA GASKIYA TA BA WALLAH, SANNAN KA SAN WACCE TA HADDACE AL’kURANI KO? TO WALLA AN CI AMANARTA KUMA ALLAH SAI YA SAKA MATA”
Ire-iren wadannan misalai suna da yawa, amma zan yi amfani da taken labarina in jawo hankalin iyaye. Wasu abokai ne guda biyu, tare suka yi firamare, sakandare da Jami’a. bayan sun sami ainkin yi da wasu shekaru sai guda yace da dan-uwansa, wallahi wane ina son in nemi Laraba, to in gajarta maka bayani, daga ranan abokantakar ta yanke. “Dan ubanka ni za ka yi wa iskanci, rainin wayo da rashin mutunci? Ka gama iskancinka da karuwai, sa’anan kace kanwata kake so. Me zai hana ka koma ka auro cikin matan da ka yi bushasha da badala da su? Amsar da ta fito daga bakinsa itace; “ai ka san na tuba” shi kuma yayan Laraba sai ya ce da shi, to mai zai hana ka nemo daya daga cikinsu, ka ba ta shawara ta tuba, in yaso ku yi aure?! Sai ya ce “Wallahi ba zan iya auren daya daga cikinsu ba”, sai yayan Laraba ya ce, to bari ka ji, yadda ba za ka iya auren daya daga cikin su ba, to haka ita ma kanwata ba zan taba bari ta aure ka ba, matukar ina raye.
To, Iyaye, ‘Yammata da samari, kun ji. Idan abokin iskanci na bazai yarda in auri kanwarsa ba, saboda bai son ya hada zuriya da mummunan iri, to kai mai zai sa ka jefa kanka ko diyarka ko dan uwanka cikin wani mummunan hali? Babban abun tsoro, bayan tsoron mahalicci Allah shi ne, mafi yawan masu wannan halin, wallahi suna dauke da cutar kanjamau.
Allah ya jikan Malam Aliyu na layinmu. Na taba neman ‘yarsa da aure, saboda wasu dalilai ya hana ni, sakamakon Allah ya rubuta ba mata t ace ba. Amma alhamdulillahi, ya cika mun burina, a lokacin da wani mai hali ya zo nemanta. Malam Aliyu,yace masa, zan baka ‘yata, amma da sharadin sai mun je wurin likitana, an yi maka gwajin cutar kanjamau. Gogan naku kuwa, tunda yana matukar son ta, sai ya aminta. Wallahi, da sakamako ya fito, abun ba dadin ji.
A yi hattara ‘yan-uwa. Domin ana samun masu wannan halin a cikin jinsin maza da mata baki daya. Amma ban sani ba ko mai karatu na iya auren daya daga cikinsu? Ni dai ban iya wa, duk da cewa ya halasta!
Za a iya tuntubar Abu Rumsa’u ta kafar sadarwa da lambobin wayar salularsa: [email protected]@gmail.com (08035081948/08027411571)