Shekarun namijin da ’yan mata suka fi so

Dalilan ’yan mata da matan aure na zabin shekarun namijin da suka fi so.

Shekarun namijin da ’yan mata suka fi so

Yawan shekarun na daga cikin abubuwan da wasu mata ke kaunar samun namiji da shi a matsayin abokin rayuwa.

Wasu ’yan mata sun fi son namijin da ya girme su sosai, saboda a ganinsu, yawan shekaru da gogewa a rayuwa babbar kadara ce, ra’ayin wasu ’yan mata kuma ya saba wa hakan.

Matan da suka fi don dattawa na ganin cewa mazan da suka manyanta ba su da zafin kai irin na matasa; Hasali ma ba lallai ba ne wanda bai dara su ba ya yi musu kwarjinin da ake bukata ga namiji.

Kazalika dattijo ya fi ba da wa mace kulawa, saboda yawan shekarunsa ya ba shi damar fahimta da kuma iya tafiyar da mace, sabanin matashi mai karancin shekaru.

Amma wasu mata matasa kuma sun bayyana cewa ba za su iya auren na mijin da ya girme su sosai ba.

A zantawarsu da Aminiya, sun ce babban dalilinsu shi ne ba za su samu walwala su wataya da dattijo ba.

Wata matar aure mai ’ya’ya biyu a Kaduna, Basma Abdul, ta ce “Tazarar shekara biyar zuwa shida haka ya yi, amma shekara 10 ko fiye da haka ya yi yawa, domin a lokacin da nake da shekaru 30 ko 40 da wani abu shi ya kai 50 ko 60 da wani abu ke nan, gaskiya ba da ni ba…”

Wata wadda ta nemi a aboye sunanta ta ce, “Idan namiji ya manyanta, akwai yadda yake daukar kansa. Akwai iya girmamawan da za ki ba shi. Da wuya ki iya jan ra’ayinsa ko shawo kansa yadda za ki yi wa wanda kanku daya ba…”

Wasu matan kuma sun nuna cewa yawa ko karancin shekarun namiji bai dada su da kasa ba.

Fatima Muhammad ta ce, “Yawan shekaru bai dame ni ba. Idan yana da hankali kuma mun dace da juna kuma mun samu fahimtar juna shi ke nan.

“Akwai matasan da suka fi wasu manyan hankali. Akwai kuma manyan da suke da yarinta da zafin kai irin na matasa. Ya danganta da irin samun fahimtar juna da aka samu…”

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano