IS na amfani da iska mai guba wajen hada bam
Kafar yada labarai ta BBC ta ga wata hujja da ke nuna cewa mayakan kungiyar IS na amfani da iskar gas mai guba ta ‘Chlorine’ a matsayin wani makami a filin daga a kasar Iraki. Gwamnatin Iraki ta ce kungiyar na amfani da wannan iska mai guba ‘yar kadan wajen hada bama-baman da ake dasawa […]
Kafar yada labarai ta BBC ta ga wata hujja da ke nuna cewa mayakan kungiyar IS na amfani da iskar gas mai guba ta ‘Chlorine’ a matsayin wani makami a filin daga a kasar Iraki.
Gwamnatin Iraki ta ce kungiyar na amfani da wannan iska mai guba ‘yar kadan wajen hada bama-baman da ake dasawa a bakin titi, da nufin kashe dakarun kasar da ke kokarin fatattakkar mayakan kungiyar daga Tikrit.
A wani bidiyon da masu kwance irin wadannan bama- bamai na Iraki suka nunawa BBC, ya nuna yadda irin wadannan bama-bamai ke fitar da wani hayaki mai kauri launin ruwar lemo zuwa sararin samaniya.
Kwararru a kan makamai masu guba sun yi imanin cewa an tsara amfani da irin wadannan bama-baman ne ba domin su yi lahani a jikin dan Adam. Sai domin su sanya tsoro a cikin zukatan jama’a.
Akwai wasu rahotanni da suke cewa kungiyar ta fara amfani da iskar ne tun cikin shekarar bara, sai dai hukumomin kasar sun wannan faifan ne kawai ya tabbatar da amfani da ita.
Wani jami’i a bangaren kwance bama-baman kasar, Haider Taher ya ce ya kwance bama-bamai da dama da suke dauke da sinadarin mai guba na Chlorine, a cigaba da yaki da kasar take da ’yan gwagwarmayar. Ya ce: “Sun fara amfani da sinadarin ne cikin bama-baman da ake hada wa a gida, wadanda idan jama’a suka shaka yake haifar masu da matsaloli.”