IS ta yanke wa mutum 1,500 haddi a wata biyar

Wata kungiyar mai sa ido wato (Syrian Obserbatory for Human Rights) ta ce kungiyar Daular Musulunci (IS) ta kashe mutum 1,500 dalili da haddin kisa da kungiyar ta yanke masu tun bayan ayyana kafa daular. kungiyar ta ce yawancin wadanda hakan ke ritsawa da su a kasar Siriya fararen hula ne. Ta kara da cewa: […]

IS ta yanke wa mutum 1,500 haddi a wata biyar
IS ta yanke wa mutum 1,500 haddi a wata biyar

Wata kungiyar mai sa ido wato (Syrian Obserbatory for Human Rights) ta ce kungiyar Daular Musulunci (IS) ta kashe mutum 1,500 dalili da haddin kisa da kungiyar ta yanke masu tun bayan ayyana kafa daular.

kungiyar ta ce yawancin wadanda hakan ke ritsawa da su a kasar Siriya fararen hula ne. Ta kara da cewa: “A cikin jimillar wadanda kungiyar IS ta kashe, 879 fararen hula ne, 700 ’yan kabilar Shaitat–’yan Sunnin daga gabashin lardin Deir El Zor lokacin da suka yaki kungiyar IS a bana. Akwai kuma mutum 63 da mambobin kungiyar al-Nusra Front ne, wadanda suma suka yaki IS a yankin arewaci da gabashin kasar. Hakazalika, akwai sojojin kasar 483 da kuma mutum hudu mambobin IS din wadanda aka kama su da aikata laifuka.”
Har ila yau, akwai wani saurayi Bafaranshe dan kungiyar IS wanda ya fito a wani faifan bidiyo, inda yake nuna sare kan wani sojan kasar Siriya da wani ma’aikacin agaji Ba’amurke, ranar Litinin da ta gabata.
An dai yi amannar cewa saurayin bai wuce shekara 22 da haihuwa ba. Kuma an bayyana sunansa da Madime Hauchard, wanda ya fito daga wani kauye a garin Normandy da ke yankin arewacin Faransa. Saurayin ya isa Siriya ne a watan Agustan bara bayan ya yada zango a Mauritaniya a shekarar 2012.