IS ta yi barazanar kashe dan kasar Japan da ta sace

Firaministan kasar Japan ya yi Allah-wadai da wani sabon hoton bidiyo da kungiyar IS ta fitar, inda suke barazanar kashe wani dan kasar mai suna, Kenji Goto cikin sa’o’i 24, idan kasar ba ta biya kungiyar diyyar dala miliyan 200 ba. Mista Shinzo Abe ya ce kasar sa tana aiki tare da Jordan domin ganin […]

IS ta yi barazanar kashe dan kasar Japan da ta sace
IS ta yi barazanar kashe dan kasar Japan da ta sace

Firaministan kasar Japan ya yi Allah-wadai da wani sabon hoton bidiyo da kungiyar IS ta fitar, inda suke barazanar kashe wani dan kasar mai suna, Kenji Goto cikin sa’o’i 24, idan kasar ba ta biya kungiyar diyyar dala miliyan 200 ba.

Mista Shinzo Abe ya ce kasar sa tana aiki tare da Jordan domin ganin mayakan kungiyar sun sako mutumin.
A cikin faifan bidiyon, an ji wata murya da aka yi amanna ta Kenji Goto ne yana cewa za a kashe shi tare da wani matukin jirgin sama dan kasar Jordan, muddin ba a saki wata ‘yar kasar Iraki da aka yanke wa hukuncin kisa a Jordan ba.
Firaministan ya kuma bukaci majalisar doko0kin kasar da ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kare ‘yan kasar da ke zaune a gida da wasu kasashen ketare.
Ita dai matar mai suna, Sajida al-Rishawi, ‘yar kungiyar al-kaeda ce, wadda mahukuntan kasar Jodarn suka yanke wa hukuncin kisa saboda hannu da take da shi a wani hari da aka kai a shekarar 2005 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 60.
A farkon makon jiya ne Mista Abe ya bukaci a gaggauta sake Japanawa biyu da aka sace, bayan ‘yan kungiyar masu jihadi sun nemi a biya su kudin-fansa.Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su tsaya tsayin-daka wajen yakar kungiyar.
Har ila yau, a shekaranjiya Laraba ne Ministan yada labaran kasar Jordan, Mohamed al-Momani, ya ce a shirye kasarsa take ta mika Sajida, ga kungiyar IS idan har kungiyar ta saki matukin jirgin nan dan Jordan ba tare da cutar da shi ba.