Isa Abba Adamu: Ba rabo da gwani ba…

“Ni kuma ni ne Isa Abba Adamu, daga nan tsakiyar birnin Landan”. Duk wanda ya kasance yana sauraron Sashen Hausa na BBC a shekarun 1990 ba zai manta da wadannan kalamai ba, ballantana mai furta su. PSG za ta sayar da ’yan wasanta 10 saboda Messi Jama’a sun kona motar kwastam da ta kashe mutane […]

Isa Abba Adamu: Ba rabo da gwani ba…

“Ni kuma ni ne Isa Abba Adamu, daga nan tsakiyar birnin Landan”.

Duk wanda ya kasance yana sauraron Sashen Hausa na BBC a shekarun 1990 ba zai manta da wadannan kalamai ba, ballantana mai furta su.

A wancan lokacin akwai zakakuran ’yan jarida irin su Umar Yusuf Karaye da Usman Mohammed da Jamila Tangaza da sauran su – wadanda ko wannensu ya yi fice a kan aikinsa, hakan kuma ya sa masu sauraro mararin jin muryoyinsu.

Amma a cikinsu babu wanda yake burge ni kamar Isa Abba Adamu.

Dalili kuwa shi ne yadda yake gabatar da shirye-shirye ko karanta labarai a lokacin, da irin salon da yake amfani da shi, sun sha bamban da na sauran abokan aikinsa; Musamman yadda yake amfani da kalaman da na ambata a sama – hakika wannan salo ya ja hankalin masu sauraro da dama.

Babu shakka wannan salo ya kayatar da ni matuka, kuma ya saka ni nishadi.

Wannan ne ya sa samun labarin rasuwar gogaggen dan jaridar ya saka ni cikin dimuwa.

Ko da yake ban taba haduwa da shi ba, a ko da yaushe ake maganar kwarewa da sanin aikin jarida, musamman a bangaren rediyo, Isa Abba Adamu nakan fara tunawa.

Wannan shi ne tasirin da marigayin ya yi, kuma wadanda suka taba sauraren shi za su ci gaba da tuna shi.

Ni dai lokaci na karshe da na samu labarin Isa Abba Adamu shi ne lokacin da aka nada shi Editan Sashen Afirka da Gabas ta Tsakiya na BBC, mukamin da aka ce shi ne bakar fata na farko da ya taba rikewa.

Kafin nan dai ya kafa tarihi a matsayin bakar fata na farko da ya zama Editan Sashen Hausa na BBC – kafin shi Turawa ne suka shugabanci sashen.

Na so a ce na hadu da Isa Abba Adamu a lokacin rayuwarsa amma Allah bai yi ba.

Hakika rashinsa ya bar wani babban gibi wanda za a dade ba a cike shi ba a harkar aikin jarida.

Da fatan Allah Ya jikan shi, Ya bai wa ’yan uwansa da sauran abokan aikinsa hakurin rashin sa.

Kamalu Garba Wali ya rubuto daga Kano.