Isah Mustapha Agwai 1 (1935 zuwa 2019)

Arewa da kuma Najeriya sun rasa daya daga cikin dadaddun sarakunansu sakamakon rasuwar Mai martaba Sarkin Lafiya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa, Alhaji Isah Mustapha Agwai 1, a ranar Alhamis 10 ga Janairun bana. Ya rasu ne a asibitin Nizamye da ke Abuja yana da shekara 84. Sarkin wanda ya fito daga gidan sarauta […]

Isah Mustapha Agwai 1 (1935 zuwa 2019)
Isah Mustapha Agwai 1 (1935 zuwa 2019)

Arewa da kuma Najeriya sun rasa daya daga cikin dadaddun sarakunansu sakamakon rasuwar Mai martaba Sarkin Lafiya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa, Alhaji Isah Mustapha Agwai 1, a ranar Alhamis 10 ga Janairun bana. Ya rasu ne a asibitin Nizamye da ke Abuja yana da shekara 84. Sarkin wanda ya fito daga gidan sarauta na Aliyu Ari, ya zamo Sarkin Lafiya na 16 ne a 1974. Ya shafe shekara 44 a gadon sarauta, inda a wannan tsakani masarautarsa ta samu sauye-sauye masu yawa a fagen siyasa da tattalin arziki.

An haifi marigayi Sarkin ne a ranar 15 ga Fabrairun 1935 a Kofar Kaura da ke Lafiya, kuma mahaifansa su ne Mumammad Al-Mustapha Marafa da Hajiya Halimatu. A farkon rayuwarsa an sanya shi a makarantar Alkur’ani a Kofar Kaura, Lafiya, inda daga baya aka sanya shi a Makarantar Elematare ta Lafiya a 1943.

Bayan kammala elemantare a 1951, Isah Mustapha Agwai ya shiga Makarantar Midil ta Katsina-Ala da ke Jihar Benuwai a yanzu. Kuma bayan kammala karatun sakandare a 1958, Isah Mustapha Agwai ya samu shiga Sashin Koyon Mulki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1958, inda ya samu Diploma a Fannin Kudi a 1959. Ya fara aiki da Hukumar En’e ta Lafiya inda ya zama Mataimakin Ma’aji, sannan jami’in tattara haraji daga baya kuma babban jami’in biyan kudi mai kula da kasuwannin En’e ta Lafiya.

Isah Mustapha ya rike mukaman gwamnati da dama, kuma ya rike sarautar Dan Galadiman Lafiya, Hakimin Obi. Bisa wannan sarauta ya zama cikakken wakili a Hukumar En’e ta Lafiya. Marigayi Sarkin wanda fadawa suke yi wa kirari da Isa Dan Halima ya taba rike Uban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, kuma har zuwa rasuwarsa shi ne Uban Jami’ar Kimiyya ta Tarayya da ke Akure a Jihar Ondo. Kuma shi Mataimakin Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa ce kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Nasarawa, sannan Mataimakin Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).

A sakonsa na ta’aziyya Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya kadu sosai lokacin da ya samu labarin rasuwar Sarkin. Ya yi ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura da Masarautar Lafiya da al’ummar Lafiya da Jihar Nasarawa dangane da rasuwar Sarkin, inda ya bayyana marigayin da Sarkin da ake matukar girmamawa.

Shugaban Kasar ya ce Gwamnatin Tarayya tana matukar tausaya musu a daidai lokacin da suke zaman makokin rasuwar Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Nasarawa kuma Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar, wanda za a ci gaba da tunawa da shi kan kyakkyawan shugabanci da sadaukar da kan da ya nuna wajen inganta rayuwar al’ummarsa.

Rasuwar Alhaji Isah Mustapha Agwai babbar asara ce ga Najeriya ba masarautarsa da Jihar Nasarawa kadai ba, ganin za a rasa irin dimbin kwarewa da kyawawan shawarwarinsa da hikimominsa da kwarewarsa kan al’amuran da suka shafi al’adu da dabi’un jama’a.

Lokacin da ya zama Sarkin Lafiya a 1974, masarautarsa tana cikin tsohuwar Jihar Benuwai da Filato ce. Yana kan gadon sarauta aka raba jihohin Benuwai da Filato a 1976. Masarautar Lafiya tana bangare da ake kira da Gangaren Filato, yankin da ya yi suna a tashe-tashen hankalin siyasa a 1979 zuwa 1983. Ba domin hikimar mutane irin su Sarki Isa Agwai ba, rikicin da ya rika faruwa a tsakanin jam’iyyun NPP da NPN da suka shaya daga a Sama da Gangaren Filato na iya haifar da zubar da jini.

Alhaji Isah ya kuma ga kirkiro Jihar Nasarawa daga Jihar Filato a 1996, kuma hedkwatar masarautarsa ta Lafiya ta kasance sabuwar hedkwatar jihar. Kuma duk da cewa sabuwar jihar tana da manyan sarakuna, Sarkin Lafiya ya kasance Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar. A kan wannan matsayi tun 1996, gwamnatocin da suka biyo baya sun ci gaba da cin ribar dimbin hikimomi da kwarewar Sarkin. Ya yi rayuwa cikin lumana da mutum uku da suka kasance gwamnonin Jihar Nasarawa bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, kuma ya yi aiki bilhakki da gaskiya wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautarsa a lokutan da ake zaman dar-dar. Allah ya gafarta masa Ya sa Aljanna ta zama makomarsa