ISIL: Iran da Saudiyya na kokarin kulla sabon kawance

Ministocin Harkokin kasashen Waje na Iran da Saudiyya sun gana a karon farko tun lokacin da aka zabi Shugaba Hassan Rouhani a bara.An ruwaito cewa mutanen biyu sun gana ne a birnin New York na kasar Amurka, inda aka ambato Ministan Harkokin Wajen Iran Jabad Zarif yana cewa ganawar na iya kasancewa wani sabon babi […]

ISIL: Iran da Saudiyya na kokarin kulla sabon kawance
ISIL: Iran da Saudiyya na kokarin kulla sabon kawance

Ministocin Harkokin kasashen Waje na Iran da Saudiyya sun gana a karon farko tun lokacin da aka zabi Shugaba Hassan Rouhani a bara.
An ruwaito cewa mutanen biyu sun gana ne a birnin New York na kasar Amurka, inda aka ambato Ministan Harkokin Wajen Iran Jabad Zarif yana cewa ganawar na iya kasancewa wani sabon babi da zai bude sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu masu gaba da juna.
Iran mai bin akidar Shi’a da kuma Saudiyya mai bin akidar Sunni sun yi hannun riga a rikice-rikicen da ake fama da su da dama da suka hada da na Syria da Iraki.
Kowacce kasa na son ganin ita ke da karfin fada-a-ji a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sai dai kasashen biyu sun gano suna fuskantar barazana guda a yanzu daga kungiyar mayakan IS da take kokarin mamaye kasashen Syria da Iraki.
A wani labarin kuma jami’an Amurka sun ce kasashen Saudiyya da Daular Larabawa da Jordan da Bahrain da katar sun shiga cikin hare-haren da ake kaiwa a Syria, sai dai ba su ce ga matsayinsu ba.
Jordan ta fitar da wata sanarwa cewa ta tura jirginta a hare-haren da ake kai wa mayakan IS domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron iyakokinta da kuma dakile shigowar masu gwagwarmaya da makaman.
Shugaban gamayyar ’yan adawar Syria, Hadi al-Bahra ya ce kasashen duniya sun hade da su a yanzu a yakin da suke yi da Kungiyar IS. Amma ya yi kira da a kara matsin lamba a kan gwamnatin Syria.