ISIS: Ana dambarwa tsakanin Indiya da Pakistan kan daliban Najeriya da aka kama

Ana dambarwa a tsakanin kasashen Indiya da Pakistan kan daliban Najeriya biyu da aka kama a kasar Indiya bisa zargin za su tsallaka Pakistan daga can su wuce Iraki don hadewa da kungiyar ISIS da ke da’awar jihadi.Jakadun kasashen Pakistani da Indiya a Najeriya ne suka yi bayanai masu sabani da juna kan matsalar, inda […]

ISIS: Ana dambarwa tsakanin Indiya da Pakistan kan daliban Najeriya da aka kama

Ana dambarwa a tsakanin kasashen Indiya da Pakistan kan daliban Najeriya biyu da aka kama a kasar Indiya bisa zargin za su tsallaka Pakistan daga can su wuce Iraki don hadewa da kungiyar ISIS da ke da’awar jihadi.
Jakadun kasashen Pakistani da Indiya a Najeriya ne suka yi bayanai masu sabani da juna kan matsalar, inda Jakadan Indiya a Najeriya, Ajjampur Ghanashyam, ya dage cewa matasan biyu daga Jihar Kano, Imran Kabeer da Sani Jamiliu, suna hanyarsu ta zuwa Pakistan ne don shiga ISIS, yayin da takwaransa na Pakistan, Laftana Janar Agha Farook (mai ritaya), ya bayyana rahoton a matsayin zuki ta malle.
Farook ya ce Indiya tana neman bata suna ne kawai, inda ya ce ba yadda za a yi daliban su iya keta iyakar kasashen biyu da ke makare da sojoji da bama-baman da aka dasa a kasa da kuma wayoyin masu kurzunu da aka hada da wutar lantarki.
Ya ce, zargin da ake yi wa matasan wani yunkuri ne na karya musu gwiwa, “saboda kawai su Musulmin Najeriya ne,” inji shi.
A makon jiya Ghanashyam ya shaida wa manema labarai cewamofishinsa, ‘yanzu yana daddalewa kafin ya bayar da biza ga ’yan Najeriya.’
Ya ce ofishin jakadancin ya damu kan yadda daliban Najeriya da ka iya barin karatunsu su je su shiga kungiyar ISIS, inda ya ce akwai dalibai dubu 59 daga Najeriya da suke karatu a Indiya, kuma kimanin dalibai dubu 30 sun kammala karatu a kasar.
Game da ko ofishinn ya canja ka’idojin biza bayan kama matasan Najeriyar biyu, Ghanashyam ya ce bai canja ba, sai dai ya ce suna taka-tsantsan wajen bayar da biza ga masu nema.
Ya ce an aba kashi 10 zuwa 15 na masu neman biza izinin zuwa kasar, inda ya ce ofishin zai dauki matakai masu tsauri don tabbatar da daliban Najeriya sun dawo gida bayan kammala karatunsu.
Ghanashyam ya ce, “Abubuwan da ake bukata don bayar da biza suna nan a intanet, kowa ya sani, amma ba z aka iya sanin abin da ke cikin zuciyar mutum ba don gano abin da yake niyyar yi ba. Idan yana da takardar dauka a makarantarmu kuma ka gan ta da idonka sai ka ba shi biza, amma yanzu dole ka yi taka-tsantsan. Ba ka sani ba, an shammace mu, yanzu dole a koma a gaya musu ku rika lura da wadannan yara ku tabbatar ba su fita daga nan da can ba, don a tabbatar sun kammala karatunsu sun shiga jirgi zuwa Najeriya.”
 Da yake karin haske kan yadda aka kama matasan biyu, jakadan ya ce, an ba su biza ne saboda sun gabatar da takardun da ake bukata ciki har da takardar daukarsu a makaranta daga wata cibiyar ilimi ta Indiya. Ya ce, “Matasan biyu sun ce suna son yin karatu ne a Bangalore, muka amince da su muka ba su biza ta dalibai. Sun tafi Bangalore a Satumban bara, sun yi shekara daya sai suka yanke shawarar shiga kungiyar ISIS, sai aka kama su a iyakar kasar Pakistan.”
Sai dai Jakadan Pakistan ya yi watsi da zargin da ake yi wa Kabeer da Jamiliu da ’yan sandan Punjab suka tsare a Indiya. Farook, wanda ya nuna wa manema labarai hotunan iyakokin Indiya da Pakistan a Abuja, ya ce babu yadda za a yi daliban biyu su shiga ISIS ta bi ta kasar Pakistan, saboda sai sun shiga kasshen uku kafin su isa Syriya, alhali za su iya isa Syriya a jirgin sama ta Turkiyya ko ta teku.
Ya ce, “Daga hotunan iyakokin kasashen