ISIS: Ana dambarwa tsakanin Indiya da Pakistan kan daliban Najeriya da aka kama (2)
biyu, za ku iya ganin ba yadda za a yi daliban su shiga Pakistan daga Indiya, domin iyakar sojoji na ba ta cikakken tsaro ga na’urorin kula da ita kuma Indiya ke tsaronta.”Ya kara da cewa: “Rahoton cewa daliban Najeriya za su je su shiga ISIS shifcin gizo ne; me ya sa rahoton ya fito […]
biyu, za ku iya ganin ba yadda za a yi daliban su shiga Pakistan daga Indiya, domin iyakar sojoji na ba ta cikakken tsaro ga na’urorin kula da ita kuma Indiya ke tsaronta.”
Ya kara da cewa: “Rahoton cewa daliban Najeriya za su je su shiga ISIS shifcin gizo ne; me ya sa rahoton ya fito daga jaridun Indiya kawai? Suna son kawai karya gwiwar daliban ne saboda su Musulmi ne ’yan Najeriya.”
Mahaifiyar Muhammadu Sani daya daga cikin daliban da aka kama, Hajiya Ladidi Jamilu, ta roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wajen ganin an sako daliban.
Ta shaida wa sashin Hausa na rediyon BBC a ranar Litinin cewa surukinta ne ya kai mata labarin cewa an kama Sani da abokin karatunsa a kan hanyarsu ta zuwa hutu a Pakistan.
“Ba mu ji komai daga gare su ba, tun lokacin, an gaya mana cewa suna yunkurin shiga ISIS,” inji ta.
Ta ce, “Muhammadu Sani ba a san shi da alaka da wata kungiyar addini ba, mutum ne mai kwazo, wannan ne ya sa bayan dan uwansa ya tafi Uganda ya yi shekara uku da shi ma sakamakon karatunsa ya fito da kyau ya yi kokarin neman tallafin karo ilimi a kasar waje. Lokacin da hakan bai samu ba, sai mahaifinsa ya yi kokari a kashin kansa ya tura shi Indiya don yin karatu. Yana can na tsawon shekara daya. Ya so ya zo gida hutu, amma saboda rashin kudi aka ce ya zauna a can sai badi.”
Dangane da ko tana da wani bayani kan danta ko dabi’unsa sun canja a waje, ta ce ba ta da masaniya kan haka. “Na dai gaya masa halin da nake ciki, ina fama da ciwon suga kuma ya ba ni shawarar zan iya neman kular likitoci a Indiya,” inji ta.
“Ina rokon Shugaban kasa ya taimake mu kan wannan lamari, ya taimaka a sako ’ya’yanmu. Ina rokon Shugaba Buhari… ban san inda zan kai kukana ba. Na mika lamarina ga Allah… Ina rokon Buhari ya taimaka min a sako wadannan yara… ba su bin wata kungiya, ko mu iyayensu, suna iya zuwa su bincike mu, ba mu da irin wannan akida mu Musulmi ne kawai,” inji ta.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Gwamnan Jihar Kano Baba Halilu dantiye game da kokarin da gwamnatin jihar ke yi kan maganar daliban jihar da aka kama Indiya, ya ce duk da cewa, “Wadannan dalibai biyu ba su cikin dalibai sama da 700 da gwamnatin Jihar Kano ta tura su karatu a kasar Indiya, iyayensu ne suka dauki nauyinsu. Duk da haka kasancewarsu ’yan asalin jihar gwamnati na duba hanyar da za ta bi ta shiga maganar. Tun daga lokacin da abin ya faru ni da kaina na yi magana da ofishin jakadancinmu da ke can kasar inda aka tabbatar mana da haka.”
Baba dantiye ya ce batu ne da ya shafi kasa da kasa kuma magana ce da ta shafi tsaro saboda haka dole sai an bi a hankali. Ya ce a yanzu haka maganar tana hannun Gwamnatin Tarayya.
Game da iyayen daliban, ya ce har yanzu ba su iya gano iyayen daliban ba, kuma ba su samu korafi daga iyayen daliban ba.
A karshe ya yi kira ga iyayen da ke son tura ’ya’yasnu karatu kasashen waje su rika jan kunnen ’ya’yansu game da yadda ya kamata su kasance a waje ba tare da sun janyo wa kansu ko iyayensu ko kasarsu abin kunya ba.
“Mu a banagarenmu muna gaya wa dalibanmu su guji yin hulda da mutanen da ba nagari ba, da za su iya jefa su cikin halin da na sani. Ya zama wajibi iyaye su nuna wa ’ya’yansu yadda ya kamata su tafiyar da rayuwarsu a kasashen waje da yadda za su guje wa mu’amala da masu munanan akidu,” inji shi.