Iska ta kashe mutum biyar, ta lalata daruruwan gidaje a Zamfara

Al’ummar unguwar Barakallahu da ke cikin garin Gusau a Jihar Zamfara sun gamu da bala’in  iskar hadari, wadda ta jefa mutane da yawa cikin mawuyacin hali, ta yi sanadiyyar mutuwar wasu kananan yara kimanin biyar kuma ta lalata daruruwan gidaje tare da wani masallacin Juma’a.Wani  daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Malam Abubakar […]

Iska ta kashe mutum biyar, ta lalata daruruwan gidaje a Zamfara
Iska ta kashe mutum biyar, ta lalata daruruwan gidaje a Zamfara

Al’ummar unguwar Barakallahu da ke cikin garin Gusau a Jihar Zamfara sun gamu da bala’in  iskar hadari, wadda ta jefa mutane da yawa cikin mawuyacin hali, ta yi sanadiyyar mutuwar wasu kananan yara kimanin biyar kuma ta lalata daruruwan gidaje tare da wani masallacin Juma’a.
Wani  daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Malam Abubakar Bawa ya bayyana wa  wakinmu cewa uku daga cikin wadanda suka rasu duk ’ya’yan mutum guda ne, wanda aka sani  da Sajen Ibrahim Ruwandoru.
Malam Bawa ya ce wani yaron da ya rasa ransa, wanda shi ma makwabcin wadanda suka rasu din ne, bayani ya nuna ya tafi makarantar islamiyya ne a wannan yammacin, sai dai bayan iskar ne iyayensa suka tsinci gawarsa a wani guri.
Saje Ibrahim, wanda ya rasa yaransa uku, yayin da Aminiya ta ziyarci gidansa, ta iske babu kowa, sai kayyayaki, gidan duk ya rushe.
Wakilinmu ya yi kokarin saduwa da shi, abin ya ci tura, amma an kira shi a waya ya dauka, sai ba a jinsa. Wata majiya da ke kusa da shi ta shaida wa wakilinmu cewa matarsa, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta tsallake rijiya da baya, domin a halin da majiyar ke bayani, tana asibiti don ta sami karaya da buguwa.
daya daga cikin wadanda iskar ta lalata gidajensu, wata mata mai sunana Lubabatu Shehu, wacce take tare da yara tara, nata biyar na makwabta hudu, a lokacin da abin ya faru, ta shaida wa wakilinmu cewa dakin da suke ciki gaba daya ya kwashe kuma ya ruguje, sai dai Allah, cikin ikonSa, babu abin da ya same su.
Sai dai wakilin namu ya lura cewa Lubabatu tana cikin matsala, domin ba ta da inda take kwana, sai gidin itaciya, kuma babu wanda ya ba ta ko da daki guda, kuma ba ta sami wani tallafi daga gwamnati ba, sai alkawarin da mataimakin gwamna ya zo ya yi musu, wanda shi ma har lokacin da ya tattauna da ita, ba ta ga komai ba, “Wallahi muna bukatar taimako matuka don ko abin da za mu ci ba mu da shi, sai wanda daidaikun mutane suka kawo mana”. Inji ta.
Da yake bayyana yana wa wakilinmu nashi bangare, mai unguwar Barakallahu, Malam Muhammadu ya ce lokacin da abin ya faru ba shi a gida, “Amma goshin magariba ne, bayan iskar ta taso, sai maidakina da ke tare da yaro mai shekara biyar, suna cikin dakin sai ya kware, gini kuma ya rufe su. Ita uwar da ta ga haka, sai ta kifu kan yaron, kamar dai yadda kaza take wa ’ya’yanta, shi kuma yaro yana kara yana ‘Mama, mama’, ita kuma tana sallallami, har dai yaro ya suke, daga bisani kafin a fito da su ya rasu. Da jama’a suka ji sallallaminta ne sai aka rugo aka kwashe bulo din aka fito da ita, amma ita ta sami raununnuka, muka kai ta asibiti”. Inji shi.
Wata majiya daga hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Zamfara (ZEMA) ta bayyana cewa lallai a halin da ake ciki yanzu ana kokarin gano wadanda abin ya shafa don ba su tallafin gaggawa. Ta kara da cewa lallai yanzu suna kokarin gano adadin gidajen da abin ya shafa. Wata majiyar kuma ta bayyana cewa akalla gidajen da suka fuskanci wannan matsalar sun kai sama da dari biyu.
Malam Atiku Sani Maradun, wanda shi ne sakataren hukumar ta ZEMA, ya bayyana wa manema  labarai cewa wannan annoba ta iska ba cikin garin Gusau kadai ta shafa ba, har ma da kananan hukumomin Tsafe da Zurmi da kuma Maradun.
Sakataren ya ce a dukkan kananan hukumomin, wasu an sami gidaje sama da hamsin, wasu kuma sama da dari da hamsin, don haka ya yi nunin cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen taimaka wa mutane don samun sauki.