Iska ta lalata turaku da wayoyin lantarki a Birnin Kudu, ta jefa dubban jama’a cikin duhu

Ƙungiyar ta yi ga kamfanin KEDCO da ya gyara wutar domin ɗorewar al’amuran jama’ar yankin.

Iska ta lalata turaku da wayoyin lantarki a Birnin Kudu, ta jefa dubban jama’a cikin duhu

Wata iska mai ƙarfi ta lalata turakun wutar lantarki da wayoyinsu a yankunan Birnin Kudu da Gwaram na Jihar Jigawa, lamarin da ya jefa dubban mazauna yankin cikin duhu.

Ƙungiyar Muryar Birnin Kudu ta ce iskar ta tumɓuke turakun wutar lantarki guda takwas tare da lalata wayoyin lantarki da ke kan layin Birnin Kudu zuwa Gwaram.

Sakamakon haka, an shafe kusan makonni biyu ba tare da wutar lantarki ba.

A wata sanarwa da Muƙaddashin Sakataren Yaɗa Labaran ƙungiyar, Malam Kabiru Zubairu, ya fitar a ranar Asabar, ya ce lalacewar turaku da wayoyin lantarkin ta shafi dubban gidaje, wuraren kasuwanci da cibiyoyin gwamnati.

Sanarwar ta ce lokacin da aka shafe babu wuta ya durƙusar da harkokin kasuwanci, inda ‘yan kasuwa da masu ƙananan sana’o’i suka dakatar da ayyukansu tare da yin asara.

Ta kuma bayyana cewa cibiyoyin lafiya, makarantu da gidaje na ci gaba da fuskantar matsaloli saboda rashin wutar lantarki.

Ƙungiyar ta buƙaci Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da ya gaggauta gyara turaku da wayoyin da iska ta lalata.

Haka kuma, ta yi kira ga shugabannin Ƙananan Hukumomin Birnin Kudu da Gwaram, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin tallafa wa aikin gyaran domin a dawo da wutar cikin gaggawa.

Ƙungiyar ta ce idan ba a gaggauta gyara turaku da wayoyin lantarkin ba, matsalar na iya ƙara shafar tattalin arziƙi da rayuwar al’ummar yankin.