Iskar gas: Rasha ta jefa kasashen Turai a tsaka mai wuya
Rasha ta ci gaba da tura iskar gas zuwa kasashen Turai, amma a wannan karon ta rage adadin, zuwa kashi 30 cikin 100 na adadin da ta saba turawa a baya.
Rasha ta ci gaba da tura iskar gas zuwa kasashen Turai, amma a wannan karon ta rage adadin, zuwa kashi 30 cikin 100 na adadin da ta saba turawa a baya.
A safiyar Alhamis bututun Nord Stream 1 ya ci gaba da aikinsa na tura makamashin iskar gas kai-tsaye zuwa kasar Jamus bayan kwana 10 da rufe shi domin aikin gyare-gyare.
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan sabon karin kudin fetur
- Malamin Lissafi ya yi wa dalibarsa illa a kashin baya da bulala
Shugaban kamfanin da ke kula da Nord Stream 1, Klaus Müller, ya sanar cewa yanzu karfin da bututun na aiki bai wuci kashi 30 cikin 100, kuma karfin da ake ta tabbaci ke nan a tsawon awa biyu.
Ya kuma bayyana cewa abu ne mai wuya karfin ya sauya a cikin kwana guda.
Adadin na yanzu ya gaza wanda Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi hasashen yiwuwar taguwar adadin zuwa kashi 33 cikin 100 a cikin kwana 10.
Hakan na zuwa ne bayan a ranar Laraba ya nuna yiwuwar kasarsa ta ci gaba da rufe bututun domin kammala aikin garambawul din shekara-shekara da take yi masa.
Tun bayan rufe katafaren bututun wanda ke tura gas kai-tsaye zuwa kasar Jamus, gwamnatin kasar ta nuna fargabar Rasha na iya fakewa da aikin gyaran wajen gallaza mata da ma daukacin kasashen Turai ta hanyar tsawaita wa’adin aikin d gangan.
Kasashen Turai dai na jiran tsammanin samun iskar gas daga Rasha, a yayin suke zargin Rashar na iya ci gaba da hana su a matsayin makamin siyasa.
“Moscow na iya amfani da hatsi da iskar gas a matsayin makamai. Dole mu dauki kwarara matakan kare kanmu,” in ji Shugabar Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz a farkon wannan mako.
Zuwa ranar Laraba Gwamnatin Jamus ta ce gas din da take dashi a ajiye ya kai kashi 65 cikin 100.