Isra’ila ba za ta sake kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran ba — Netanyahu
Wannan na zuwa ne biyo bayan gargaɗi da Trump ya yi wa Isra’ila kan kai wa cibiyoyin makamashin Iran hari.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da cewa ƙasarsa za ta dakata da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran.
Wannan mataki ya biyo bayan gargaɗin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Isra’ila na cewa kada ta sake kai irin wannan hari.
- FIFA ta ce za a gudanar da Gasar Kofin Duniya duk da rikicin Iran
- Sallah: Sanusi II ya buƙaci Musulmi su ɗore kan kyawawan ɗabi’un da suka koya a Ramadan
A ranar Laraba, Isra’ila ta kai hari kan wata babbar cibiyar sarrafa iskar gas ta Iran mai suna South Pars, lamarin da ya sa Iran ma ta mayar da martani.
Waɗannan hare-hare sun haddasa tashin farashin man fetur da iskar gas a kasuwannin Turai da ma duniya baki ɗaya.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, Netanyahu ya tabbatar da cewa: “Ba za mu sake kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran ba.”
Haka kuma, ya ƙaryata zargin da ake yi na cewa shi ne ya zuga Trump ya kai hari kan Iran.
Ya bayyana cewa: “Babu wanda zai iya faɗa wa Shugaba Trump abin da zai yi. Shi kansa yana yanke shawara ne bisa abin da ya ga ya dace.”
Ya ƙara da cewa: “Shugaba Trump yana ɗaukar matakai ne domin maslahar Amurka da kuma makomar duniya baki ɗaya.”