Isra’ila da Falasdinu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
Masar ta bukaci bangarorin biyu su kiyaye tare da aiwatar da bin ka’idojin yarjejeniyar.
Isra’ila da kungiyar ’yan gwagwarmaya ta Falasdinu a zirin Gaza sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan shafe kwanaki biyar ana arangama.
Wannan dai wani yunkuri ne domin kawo karshen arangamar da ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa 33 da suka hada da kananan yara da kuma mutane biyu a Isra’ila.
- Rikicin makiyaya da manoma ya yi ajalin mutum 38 a Nasarawa
- Ina neman yafiyar magoya bayan Arsenal kan shan kaye a hannun Brighton —Arteta
Yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki ne bayan da kasar Masar ta shiga tsakani.
Gabanin tsagaita wutar, an samu musayar wuta da rokoki a cikin mintuna na karshe da kuma hare-haren da Isra’ila ta kai na tsawon mintuna da dama da suka wuce wa’adin.
Wani jami’in kungiyar Falasdinu ya ce rawar da Masar ta taka na shiga tsakani na da matukar muhimmanci wajen cimma wannan yarjejeniya.
Yarjejeniyar dai ta hada da tsagaita bude wuta da Isra’ila da Falasdinawa suka yi da kuma kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula da gidaje.
Masar ta bukaci bangarorin biyu su kiyaye tare da aiwatar da bin ka’idojin yarjejeniyar tsagaita bude wutar.
Sai dai yarjejeniyar ba ta tabo batutuwan da suka haifar da yakin baya-bayan nan tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa a zirin Gaza ba.