Isra’ila da Iran na neman a gaggauta tsagaita wuta — Trump
Trump dai na ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikicin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Amurka.
Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Isra’ila da Iran na neman cimma yarjejeniyar tsagaita wuta cikin gaggawa, bayan da ƙasashen biyu sun sake kai wa juna hare-hare karo na farko tun bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma watanni biyu da suka gabata.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social, inda ya ce ɓangarorin biyu suna son a dakatar da yaƙin nan take.
- MDD ta fara bincike kan zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya
- Dalilin da na fasa sako matar Janar Rabe — Ɗan bindiga
Ya kuma ce tattaunawa kan samar da zaman lafiya na ci gaba da gudana, sai dai ya gargaɗi ɓangarorin da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas a sulhun da ake ƙoƙarin yi.
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan Trump ya buƙaci Isra’ila da Iran su dakatar da hare-haren da suke kaiwa juna nan take.
Rahotanni sun ce Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila a daren Lahadi zuwa safiyar Litinin, yayin da Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wasu wuraren soji a Iran.
Harin na Iran ya biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan wuraren da ake dangantawa da ƙungiyar Hezbollah a kudancin birnin Beirut.
Trump dai na ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikicin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Amurka yayin da ake tunkarar zaɓukan rabin wa’adi da za a gudanar nan gaba.