Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta
Kasar Iran ta zargi Isra’ila da kai mata hari a safiyar Talata bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta
Kasar Iran ta zargi Isra’ila da kai mata hari a safiyar Talata bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu.
“Gwamnatin Yahudawa ta ƙaddamar mana da hari har guda uku a ƙasar Iran har zuwa ƙarfe 9:00 na safiyar Talata,” kamar yadda gidan talabijin ɗin kasar Iran ya ambato Kakakin rundunar sojojin ƙasar yana faɗa.
- Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara
- DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Kafin sanar da tsagaita wutar dai duka bangarorin biyu sun kai wa juna munanan hare-hare cikin dare.
’Yan mintina kafin lokacin ya cika dai, makaman Iran masu linzami sun sauka a kan wani gida da ke birnin Beersheba na kudancin Isra’ila, inda ya kashe mutum huɗu.
Sojojin Isra’ila sun ce sun game makaman daga Iran aka harba su.
Rundunar tsaron Isra’ila (IDF) ta ce na’urorinta na aiki tarwatsa wasu makaman da aka harbo mata daga Iran, inda ta umarci mutane da su biya a cikin gidaje har zuwa abin da hali ya yi.
To sai dai Iran ta musanta kai harin.
Isra’ila dai ya sha alwashin mayar da martani kan abin da ta kira saba alkawarin yarjejeniyar da aka cimma.
A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Shugaban Trump ya ce kasashen biyu sun amince su dakatar da yaƙin cikin sa’o’i 24, inda ƙasar Iran za ta fara aiki da tsagaitawar.
Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na diflomasiyya da zai kawo ƙarshen ci gaba da lalata yankin na Gabas ta Tsakiya.