Isra’ila da Palasdinawa sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokaci

Mahukuntan kasar Masar sun ba da sanarwar cewa wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta tsawon lokaci ta fara aiki a tsakanin Palasdinawa da kasar Isra’ila.Kuma jami’an Isra’ila da na Palasdinawa sun tabbatar da cewa an cimma wannan yarjejeniya ta dakatar da bude-wutar, a tattaunawar da aka yi a Alkahira a ranar Talata.Shugaban Palasdinawa, Mahmud […]

Isra’ila da Palasdinawa sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokaci
Isra’ila da Palasdinawa sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokaci

Mahukuntan kasar Masar sun ba da sanarwar cewa wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta tsawon lokaci ta fara aiki a tsakanin Palasdinawa da kasar Isra’ila.
Kuma jami’an Isra’ila da na Palasdinawa sun tabbatar da cewa an cimma wannan yarjejeniya ta dakatar da bude-wutar, a tattaunawar da aka yi a Alkahira a ranar Talata.
Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas ya kara tabbatar da wannan al’amari tare da bayyana cewa “Da misalin karfe bakwai daidai agogon GMT wannan yarjejeniya ta fara aiki. Kuma dukkan bangarorin da abin ya shafa za su koma Alkahira don kammala daidaitawa.”
An yi ta murna a Gaza bayan sanar da wannan yarjejeniyar, wadda kungiyar Hamas ta ce jajircewarta ce ta kai ga wannan nasara.
Amma Isra’ila ta ce an tsara wannan yarjejeniyar sama da wata guda, kuma da Hamas ta amince tun da wuri da mutane da dama ba su hallaka ba.
Yarjejeniyar dai za ta ba da dama a bude iyakokin Gaza don shigar da kayan agaji da na gini.
Sama da mutune dubu biyu ne suka mutu mafi yawansu Palasddnawa cikin kwana hamsin da aka aka kwashe ana fada a tsakanin bangarorin biyu. Sannan Isra’ila ta lalata gine-gine da dama ciki har da masallatai 171 a Gaza, inda 71 daga cikinsu suka ruguje warwas.