Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

An kashe Mahmoud Abu Wafah, mataimakin ministan harkokin cikin gida a Gaza.

Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta inda ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Sabbin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar sun kashe fiye da mutum 200 ciki har da mata da yara tare da jikkata daruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti.

Hamas ta ce Isra’ila ta kai harin na ba-zata ne kan fararen hula da ta shammata a ƙoƙarin ta na keta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka ƙulla tun a ranar 19 ga watan Janairu.

Kazalika, dakarun tsaron Isra’ila (IDF) sun ce sun kai hari kan abin da suka kira wuri mai ‘barazanar ta’addanci’ na Hamas.

Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai a Gaza tun bayan da aka fara tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Janairu yayin da aka gaza cimma matsaya a tattaunawar tsawaita wa’adin tsagaita wutar na Gaza..

Bayanai sun ce galibin waɗanda hare-haren suka rutsa da su mutane da ke cin abincinsu na Sahur kafin fitowar alfijir.

Majiyoyi sun ce sama da jiragen yaƙin Isra’ila 20 ne suka yi shawagi a sararin sama, sannan suka soma luguden wuta a garuruwan Gaza da Rafah da Khan Younis.

Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Isra’ila Katz ne suka ba da umarnin kai hare-haren a safiyar ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Firayim Minista ta sanar.

BBC ya ruwaito cewa an kashe Mahmoud Abu Wafah, mataimakin ministan harkokin cikin gida a Gaza kuma babban jami’in tsaron Hamas a yankin.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce kawo yanzu aƙalla Falasɗinawa 48,572 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 112,032 suka jikkata a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sabunta alƙaluman waɗanda suka mutu zuwa fiye da 61,700, yana mai cewa dubban Falasɗinawa da suka bace a ƙarƙashin baraguzan ginin ana kyautata zaton sun mutu.

Aƙalla mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila a harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023, sannan sama da 200 aka kama.