Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

UNICEF ta ce yaƙin ya hana gomman yara zuwa makaranta da kuma raba su da muhallansu.

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa akwai ƙananan yara sama da 400,000 da Isra’ila ta ɗaiɗaita a Lebanon, ta hanyar hare-hare ciki mako uku.

A daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da sunan yaƙi da dakarun Hezbollah, UNICEF ta ce rayuwar dubban ƙananan yara na ci gaba da faɗawa cikin hatsari.

Asusun ya ce hare-haren sun tilasta wa yaran barin matsugunansu don tsira da rayukansu.

Mataimakin Babban Daraktan UNICEF a ɓangaren ayyukan jin-ƙai Ted Chaiban, ya yi gargaɗin cewa wannan yaƙi da Isra’ila ta faro a Lebanon kai-tsaye ya lalata tsarin ilimin ƙasar bayan da ya tilasta wa yara aƙalla miliyan 1.2 barin makarantu.

A cewar jami’in galibin makarantun da ke wannan yanki sun fuskanci hare-hare daga Isra’ila wanda ko dai ya lalata su ta yadda ba za a iya karatu ba ko kuma ya firgita yaran da ke yankin.

UNICEF ta ce akwai aƙalla asibitoci 12 da hare-haren Isra’ilar ya shafa a yankin na kudancin Lebanon mai iyaka da Isra’ila wanda ya jefa rayuwar gomman ƙananan yara cikin hatsari.

Kawo yanzu sama da mutum 2,300 ne Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta ke kai wa Lebanon da kaso mai yawa na mata da ƙananan yara.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa