Isra’ila ta bukaci Falasdinawa miliyan 1.1 su fice daga Gaza

Sai dai Hamas ta bukaci a kwantar da hankula

Isra’ila ta bukaci Falasdinawa miliyan 1.1 su fice daga Gaza

Wasu Falasdinawa a Gaza

Kasar Isra’ila ta bayar da umarnin kwashe dukkan fararen hular da suke a birnin Gaza da kuma Arewacin Zirin saboda za ta fara ruwan wuta a kan Falasdinawa.

Umarnin na zuwa ne ranar Juma’a, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya take cewa Isra’ila ta gargade ta da ta kwashe mutum miliyan 1.1 da suke Zirin na Gaza nan da awa 24.

Hakan na zuwa ne yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin kungiyar Hamas ta Falasdinawa da Isra’ila ya shiga rana ta bakwai.

Sojojin Isra’ila dai sun yi zargin cewa dakarun Hamas na buya a cikin fararen hula a birnin na Gaza.

A wata sanarwa da sojojin na Isra’ila suka ba fararen hula, sun ce, “Saboda amfaninku muke bayar da wannan shawarar.

“Za ku sami damar sake komawa Gaza ne kawai lokacin da muka bayar da umarnin yin hakan. Kada ku kuskura ku tsallaka shingen da Isra’ila ta kafa,” in ji sanarwar.

Sojojin sun kuma ce a ’yan kwanaki masu zuwa za su ci gaba da ruwan wuta a yankin, amma sun ce za su iya bakin kokari wajen ganin hakan bai shafi fararen hula ba.

Sama da mutum 1,500 ne dai kasar Isra’ila ta kashe tun bayan fara rikicin a Zirin Gaza, galibinsu mata da kananan yara.

Sai dai tuni kungiyar Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila inda ta kira shi da farfagandar karya.

Kazalika, Hukumar da ke Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Hamas ta bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar wuta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan