Isra’ila ta ce Iran ta fi IS hadari
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kasar Iran a matsayin wata babbar barazana ga kasashen duniya fiye da mayakan kungiyar IS masu da’awar kafa daular Musulunci.A jawabinsa a gaban Babban Taron Zauren Majalisar dinkin Duniya, Mista Netanyahu ya ce bai kamata a kyale Iran ta rika sarrafa Nukiliya ba, domin za ta iya kera makaman […]
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kasar Iran a matsayin wata babbar barazana ga kasashen duniya fiye da mayakan kungiyar IS masu da’awar kafa daular Musulunci.
A jawabinsa a gaban Babban Taron Zauren Majalisar dinkin Duniya, Mista Netanyahu ya ce bai kamata a kyale Iran ta rika sarrafa Nukiliya ba, domin za ta iya kera makaman kare dangi da shi. Ya kuma ce: “Ina da tabbacin cewa za a samu nasara kan kungiyar IS, amma idan aka bar Iran ta mallaki makamin Nukiliya to fa da sauran rina a kaba. kungiyar IS da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas rassa ne na wata itaciya guda da ke dauke da guba. Kuma dukkansu suna kama da jam’iyyar Nazi ta kasar Jamus lokacin Yakin Duniya na Biyu. ”
Sai dai jakadan Iran a Majalisar dinkin Duniya, Jabad Safaei, ya ce wadannan kalamai ba su cancanta ba, sai kuma ya bayyana Isra’ila da wata kasa da ta yi kaurin suna wajen tara muggan makamai da suka hada da makaman kare dangi.
Mista Safaei ya ce: “Isra’ila da tayi kaurin suna a aikata manyan laifuka, da kowa ya sani harda Majalisar dinkin Duniya, saboda haka bai kamata ta samu bakin zargin wasu kasashe ba,” inji shi.