Isra’ila ta ce Iran ta fi IS hadari

A kwanakin baya ne Hukumar Sojan Najeriya ta zartar wa wasu jami’anta hukuncin kisa, a sakamakon samun su da laifin yin bore ga kwamandansu. Wasu na ganin cewa hukuncin kisan ya yi tsauri, wasu kuma na ganin cewa ya dace a yi musu afuwa, kada a kashe su. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]

Isra’ila ta ce Iran ta fi IS hadari
Isra’ila ta ce Iran ta fi IS hadari

A kwanakin baya ne Hukumar Sojan Najeriya ta zartar wa wasu jami’anta hukuncin kisa, a sakamakon samun su da laifin yin bore ga kwamandansu. Wasu na ganin cewa hukuncin kisan ya yi tsauri, wasu kuma na ganin cewa ya dace a yi musu afuwa, kada a kashe su. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a kashe su ko kuwa a yi musu afuwa? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan mutane daban-daban:

 

Zartar da wannan hukunci zalunci ne – Baninge

Hussaini Isah a Jos

Dokta Ibrahim Baninge: ‘’A gaskiya ni a nawa ra’ayin, ya kamata a yi wa wadannan sojoji afuwa, kada a zartar musu da wannan hukunci na kisa da aka yanke musu. Domin akwai sojoji da dama da suka aikata laifuffuka na kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a jihohin Barno da Yobe da Adamawa amma ba a yi musu komai ba. Don haka ni a ganina zartarwa da wadannan sojoji wannan hukunci rashin adalci da zalunci ne. Saboda wadannan sojoji sun kawo hujjar cewa wannan kwamanda ya ba su umarnin da ba za su iya aikatawa ba ne.”

A yi wa wadannan sojoji afuwa – Habibu Nalele

Hussaini Isah a Jos

Alhaji Habibu Nalele: ‘’Ni a nawa tunanin, wannan hukunci da aka yanke wa wadannan sojoji ba a yi adalci ba. Dalili kuwa shi ne, su wadannan sojoji sun fadi dalilan da suka sanya suka kai wa wannan kwamanda nasu hari. Don haka ni ina ganin ya kamata a yi musu afuwa, a dawo da wannan hukunci zuwa dauri maimakon kisa. Wadannan sojoji ba su aikata wa wani laifi ba, manyan sojojin da suke jagorancin wannan yaki ne suke aikata laifi. Amma kananan sojoji suna iyakar bakin kokarinsu don kawo zaman lafiya kan wannan yaki da ake yi. Don haka babu hujjar da za ta sanya a zartar musu da hukuncin kisa.  Don haka ya kamata a yi musu afuwa.

Bai kamata a kashe sojojin ba – Kabiru Muhammad

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Alhaji Kabiru Muhammad: “A gaskiya bai kamata a yi aiki da hukuncin kisa ga wadannan sojoji ba. Kamata ya yi a yi musu afuwa. Idan aka lura da irin halin da wadannan sojoji suke ciki a lokacin da suka aikata laifin, suna cikin filin daga ne da suke yin aikin tserar da Najeriya daga fadawa cikin rudani da wasu makiya kasa, ’yan Boko Haram suke so su yi. Wannan dalili kadai ya isa a dauki matakin sassauta wannan hukunci; a dawo da shi zuwa daurin shekaru kadan.”

Ya kamata a yi musu afuwa – Bello Ibrahim

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Bello Ibrahim: “Ya kamata a yi wa wadannan sojoji afuwa saboda kokarin sadaukar da kansu da suka yi da yawan shekarun da suka yi a cikin aikin bauta wa kasar haihuwarsu. Duk da yake na amince da tsarin hukumomin sojan Najeriya da suka kafa kotunansu daban domin hukunta dukkan sojan da aka same shi da laifi, sai dai irin wannan hukunci ya yi tsanani. Ina rokon Shugaba Goodluck Jonathan, yayi musu ahuwa.”

Ya dace a kashe wadannan sojojin – Nata’ala Babi

Nasiru Bello, a Sakkwato

Nata’ala Babi: “Hakika kashe wadannan sojojin ya yi daidai, a kan dalilai kamar haka: Na daya, kasancewar yadda ake sukar Najeriya a sauran kasashen duniya, na cewar ba a hukunta masu laifi a wannan kasar. Ka ga wannan zai dawo da martabarmu ga idanun duniya. Na biyu idan har wannan hukuncin shi ne daidai to babu laifi a aiwatar da shi. Sai dai kuma a binciko sauran masu laifi, wadanda suka yi sanadin tayar da hankali a wasu wurare a wannan kasar kuma har ya yi sanadiyar salwantar rayuwa da dukiyoyin talakawa da dama. Domin idan aka bincika, akwai wadanda suka fi wadannan laifi tsakanin sojoji da farar hula amma aka fita batunsu, kasancewar wai su manaya ne ko kuma sun kasance wadanda suke shafaffu da mai. Idan aka ci gaba da bincika ire-irensu ana hukunta su, za a rage daukar doka a hannu kuma za a rage ta’addanci da ake yi a wannan kasar. Allah Ya ba mu zaman lafiya a kasarmu, Ya ci gaba da bayyana masu laifi da tona musu asiri. Wadanda kuma suka rasa rayukansu ba su ji ba ba su gani ba, Allah Ya yi gafara gare su.”

Bai dace a kashe su ba – Baban Umma

Nasru Bello, a Sakkwato

Baban Umma: “Maganar gaskiya, kashe wadannan sojojin bai dace ba saboda duk wanda ya san abin da ya faru to ba zai ga laifinsu ba, don zuciya ba ta da kashi; ranka in ya baci komai kana iya aiwatarwa sai dai daga baya ka yi da ka sani. Abin da ya faru ke nan ga wadannan bayin Allah. Ya kamata dai a yanke masu wani hukunci amma ba na kisa ba. Iyayensu da ’ya’yansu da abokansu na nan kuma suna bukatarsu kamar yadda ake bukatar wanda ya yanke musu hukunci. Kan haka ya kamata a sassauta wannan hukuncin zuwa wani abu daban sabanin wannnan mai tsaurin. In don kuskure sun yi amma dai in an bi ta barawo, a bi ta mai bin sawu; a cewar Bahaushe.”