Isra’ila ta dawo da hare-harenta a Gaza
Da sanyin safiyar Juma’a ta Isra’ila ta fara luguden wuta a Zirin Gaza inda ta kashe mutane akalla 21 ta jikkata wasu da dama, galibi mata da kananan yara.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Zirin Gaza daidai lokacin da Sakataren Wajen Amurka, Anthony Blinken, da ke ziyara a Tel Aviv ke cewa ya kamata Isra’ilar ta bai wa fararen hula kariya a hare-harenta a yankin Falasdinawa.
A safiyar Juma’a ne sojojin na Isra’ila suka fara luguden wuta a yankunan Rafah da Kudancin Gaza inda ma’aikatar lafiyar Falasdinu ke cewa sojojin sun kashe mutane 110, sun jikkata wasu masu tarin yawa, galibi mata da kanaan yara.
Hakan na zuwa ne bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila ba tare da sanarwar tsawaitawa ko kuma yarjejeniya ta dindindin ba.
al’ummar Gaza sun ce tun kafin karewar yarjejeniyar tsagaita wutar da misalin karfe 7 na safe suka jiyo karar harbe-harbe da abubuwan fashewa.
- Khadijah Mai Numfashi ta tuba bayan dakatar da ita daga Kannywood
- Za a fara yi wa masu fyaɗe dandaƙa a Kaduna
Sun kara da cewa tun farko sai dai Isra’ila ta girke dakaru na musamman da ke zaman jiran lokaci don ci gaba da kashe-kashe a yankin na Falasdinu.
Yankunan da hare-haren na Isra’ila suka shafa sun kunshi Arewaci da Tsakiyar Zirin Gaza da Khan Younis da kuma Rafah.
Zuwa yanzu Isra’ila ta rushe kashi 60 na gine-ginen da ke yankin na Zirin Gaza.
MDD ta yi Allah-wadai
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da sabbin hare-haren na Isra’ila tana mai bayyana shi a matshin bala’i.