Isra’ila ta gargadi Falasdinawa da su fice daga Gaza
kasar Isra’ila ta gargadi al’ummar Falasdina da ke zaune a gabashi da arewacin zirin Gaza da su fice daga gidajensu a ci gaba da kaddamar da hare-hare da take ta sama a yankin.Wannan na zuwa ne bayan kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka gudanar ranar Talata tsakanin Isra’ila da kungiyar Falasdina ta Hamas wadda […]

kasar Isra’ila ta gargadi al’ummar Falasdina da ke zaune a gabashi da arewacin zirin Gaza da su fice daga gidajensu a ci gaba da kaddamar da hare-hare da take ta sama a yankin.
Wannan na zuwa ne bayan kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka gudanar ranar Talata tsakanin Isra’ila da kungiyar Falasdina ta Hamas wadda mayakanta ke harba rokoki cikin Isra’ila. Kodayake jami’an Falasdina sun bayyana cewa sun rasa mutum fiye da 200 a rikicin, ciki har da mutum 10 ga aka kashe tsakar dare da kuma wasu yara su hudu wadanda suka mutu shekaranjiya Laraba.
Tun farko kungiyar Hamas ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar, amma wani jami’i daga bisani ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa za su duba hanyar kawo karshen rikicin a siyasance.
A ranar Talata da ta gabata ne dai Isra’ila ta ba da rahoton mutuwar Bayahude farko a rikicin. Bugu da kari ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza na zuwa ne bayan da Firaministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu ya ce ba suda wani zabi illa kara zafafa hare-harensu.