Isra’ila ta hallaka Falasdinawa 9 a Jenin

Isra’ila ta kuma ce ta lalata wani wajen horar da dakarun Falasdinawa

Isra’ila ta hallaka Falasdinawa 9 a Jenin

Harin Isra’ila a Jenen, Falasdinu. Hoto: Aljazeera

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da wani hari ta sama kan sansanin marasa galihu na Falasdinawa da ke Jenin a Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda suka hallaka mutum tara.

Kimanin mutum takwas ne dai aka kashe a hare-haren na karshen mako, na taran kuma ya rasu ranar Litinin a birnin Ramallah, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta tabbatar.

Kazalika, ma’aikatar ta kuma ce an raunata wasu sama da mutum 20 a sansanin, yayin da wasu daga cikinsu kuma yanzu haka ke cikin mawuyacin hali.

Mazauna yankunan sun ce Isra’ila ta kai hare-hare sama da 10 cikin daren Litinin, lamarin da ya sa hayaki ya turnuke ginin da suka riga suka ragargaza.

Bugu da kari, wasu gwamman sojojin na Isra’ila dauke da muggan makamai sun mamaye sansanin ta kasa, inda suka rika kai hari su ma, lamarin da ya janyo lalata gidaje da hanyoyi.

Hare-haren na ranar Litinin na zuwa ne bayan rikici ya barke a Gabar Kogin, ciki har da harin jirgi mara matuki, irinsa na farko da Isra’ila ta kai yankin tun shekara ta 2006.

A cikin wata sanarwa da Rundunar Sojojin Isra’ilar ta fitar, ta ce daya daga cikin hare-haren nasu ya lalata wata cibiyar bayar da horo da ake amfani da ita wajen horar da dakaru daban-daban daga yankunan Falasdinawa.