Isra’ila ta hana wadanda ba Musulmi ba shiga Masallacin kudus

Mahukunta a kasar Isra’ila sun hana Yahudawa da sauran wadanda ba Musulmi ba shiga Masallacin birnin kudus, har sai bayan an kammala azumin watan Ramadan.An dauki matakin ne bayan kwashe kwana biyu ana arangama tsakanin masu ibada da kuma ’yan sandan kasar Isra’ila, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta bayyana.A ranar Lahadi aka […]

Isra’ila ta hana wadanda ba Musulmi ba shiga Masallacin kudus
Isra’ila ta hana wadanda ba Musulmi ba shiga Masallacin kudus

Mahukunta a kasar Isra’ila sun hana Yahudawa da sauran wadanda ba Musulmi ba shiga Masallacin birnin kudus, har sai bayan an kammala azumin watan Ramadan.
An dauki matakin ne bayan kwashe kwana biyu ana arangama tsakanin masu ibada da kuma ’yan sandan kasar Isra’ila, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta bayyana.
A ranar Lahadi aka shiga goman karshen na watan Ramadan, kuma a wannan lokacin ne Musulmi suke tururuwan ziyartar masallacin, wanda shi ne na uku mafi daraja a duniya.
kungiyar Agaji ta Red Cross reshen Palasdinu wato Red Crescent ta ce a ranar Lahadin jami’anta sun kai Palasdinawa bakwai wani asibiti da ke  Gabashin birnin kudus saboda wasu raunukan harbi da suka ji.
Wani jami’in Palasdinawa ya ce rikicin ya fara ne lokacin da Isra’ila ta bar wasu Yahudawa masu ziyara shiga harabar masallacin, abin da ya saba wa al’adar da ake bi ta barin Musulmi masu ibada kawai su shiga masallacin yayin ranakun goman karshen na watan azumi.
Kewayen Masallacin kudus shi ne wuri da ya fi dadewa a Gabashin birnin kudus, wurin da kasar Isra’ila ta kwace a shekarar 1967, a wani mataki da kasashen duniya suka ki amincewa da shi.
Sai dai Isra’ila ta amince cewa Yahudawa da kuma wadanda ba Musulmi ba, za su iya ziyarta masallacin a wannan lokaci, amma an haramta musu yin ibada.