Isra’ila ta haramta wa Falasdinawa yin cudanya da Yahudawa a mota
kasar Isra’ila ta haramta wa Falasdinawa yin cudanya da Yahudawa a cikin mota guda a yayin da suke kokarin zuwa wajen aiki ko dawowa gida a Gabar Yamma na Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. A karkashin tsarin da Isra’ila ta kaddamar a shekaranjiya Laraba, Falasdinawan da suke shiga Isra’ila da takardun shaidar izini don […]
kasar Isra’ila ta haramta wa Falasdinawa yin cudanya da Yahudawa a cikin mota guda a yayin da suke kokarin zuwa wajen aiki ko dawowa gida a Gabar Yamma na Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. A karkashin tsarin da Isra’ila ta kaddamar a shekaranjiya Laraba, Falasdinawan da suke shiga Isra’ila da takardun shaidar izini don zuwa kwadago ba su da ’yancin shiga mota guda tare da Yahudawa.
Ministan Tsaron Isra’ila Moshe Yaalon ya ce wannan mataki ne na tsaro da zai ba su damar kula da Falasdinawan da suke shiga kasar ba tare da sun yi cudanya da Yahudawa ba.
Bayan daukar matakin, rahotanni sun ce ’yan sandan Isra’ila sun bindige wani Bafalasdine bayan ya auka wa ’yan sandan da mota tare da raunata biyu daga cikinsu a birnin kudus a shekaranjiya Laraba.
Bayan kafa sabuwar gwamnati a Isra’ila, Majalisar dinkin Duniya ta ce za ta nemi gwamnatin kasar ta gaggauta komawa kan teburin tattaunawa da Falasdinawa da nufin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Manzon Majalisar a yankin Gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenob, ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar cewa, akwai gagarumin aiki a gaban kasashen duniya wajen ganin an sake farfado da tattaunawa a tsakanin Falasdinawa da Yahudawan, bayan rugujewar tattaunawar a cikin watan Afrilun bara.