Isra’ila ta kaddamar da gasar Baibul a Najeriya
Kasar Isra’ila ta fara rajistar masu son shiga gasar Baibul ta Kasa Karo na Uku a Najeriya. Jami’a mai kula da Hukumar Raya Kasashe ta Isra’ila (MASHAV) a ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya, Chikadibia Kene-meenu, ta sanar da haka ranar Laraba a Abuja. COVID-19: Yadda Kiristoci suka yi bukukuwan Easter a gida Gasar Aminiya: […]
Kasar Isra’ila ta fara rajistar masu son shiga gasar Baibul ta Kasa Karo na Uku a Najeriya.
Jami’a mai kula da Hukumar Raya Kasashe ta Isra’ila (MASHAV) a ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya, Chikadibia Kene-meenu, ta sanar da haka ranar Laraba a Abuja.
- COVID-19: Yadda Kiristoci suka yi bukukuwan Easter a gida
- Gasar Aminiya: An fara tace labarun ’yan takara
“Wata sabuwar dama ta bude ta yin rajista don shiga gasar daga yanzu har zuwa ranar 12 ga watan Agusta.
“Ranar 13 ga watan Agusta kuma za a yi gwaji ta intanet a fadin Najeriya.
A cikin kasa da sa’a guda bayan kammala gwajin kuma za a tura wa wadanda suka yi shi rariyar likau (wato link) ta jarrabawar.
“Za a zabi mutum biyu da suka fi yawan maki daga ko wacce jiha don su fafata a mataki na gaba”, inji ta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato ta tana cewa an dauki nauyin ziyarar wadanda suka yi nasara a gasar baya zuwa Isra’ila, inda suka ziyarci wurare masu tsarki sannan suka bakunci Gasar Baibul ta Birnin Kudus.
A kan shirya gasar ne dai ta intanet duk shekara yayin da ake karawa ta karshe a Abuja.