Isra’ila ta kafa dokar daurin shekara guda ga bakin hauren Afirka
Majalisar kasar Isra’ila ta amince da dokar daurin shekara guda ga bakin haure ’yan Afirka, ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba, kamar yadda aka bayar da sanarwa tun a Larabar da ta wuce.Sabuwar dokar, wadda ta samu goyon bayan ’yan majalisa 30 da suka kada mata kuri’a, ta samu rinjaye […]
Majalisar kasar Isra’ila ta amince da dokar daurin shekara guda ga bakin haure ’yan Afirka, ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba, kamar yadda aka bayar da sanarwa tun a Larabar da ta wuce.
Sabuwar dokar, wadda ta samu goyon bayan ’yan majalisa 30 da suka kada mata kuri’a, ta samu rinjaye a kan mutum 15 da suka ki amincewa da ita, a majalisa mai mutum 120, da ake yi wa lakabin Knesset.
Wannan shi ne matakin baya-bayan nan da aka dauka a kasar don shawo kan bakin haure ’yan afirka da ke kwararowa cikin kasar ba bisa ka’ida ba, al’amarin da Gwamnatin Isra’ila ke ganin barazana ce ga kasarta.
A bara isra’ila ta kai farmakin kan bakin hauren, inda ta kama kimanin mutum dubu 60, ta kuma kora wasu har mutum dubu uku da 920 zuwa kasashensu; sannan ta gina shingen waya a twsakanin kasarta da Masar.
Tun a ranar 24 ga watan Nuwambar bana aka tabbatar da wannan doka, don magance kwararowar bakin haure, wadanbda suka hada da ’yan kwadago. Kuma gwamnatin kasar ta kuduri aniyar bayar da tallafin kudi ga wadanda suka amince su koma kasashensu.
Gwamnatin Isra’ila ta zuba kudi tsagwagwa don gina babban kurkukun tsare bakin haure don tsare bakin haure da ke kwarara kasar, da kuma wadanda ke zaune a cikinta, ta yadda “ba za su hargitsa al’umma ba,” a cewar sanarwar da ta fito daga ofishin Firayiminista.