Isra’ila ta kai hari wata kasuwa da ke Gaza
Hukumomin Falasdinawa sun bayyana cewa akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu wasu kuma kimanin 160 sun samu raunuka bayan wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a wata kasuwa da ke kusa da birnin zirin Gaza.Kasuwar tana yankin Shejaiya ne inda daruruwan jama’a ke zuwa don yin sayayya kamar yadda kakakin ma’aikatar lafiyar […]
Hukumomin Falasdinawa sun bayyana cewa akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu wasu kuma kimanin 160 sun samu raunuka bayan wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a wata kasuwa da ke kusa da birnin zirin Gaza.
Kasuwar tana yankin Shejaiya ne inda daruruwan jama’a ke zuwa don yin sayayya kamar yadda kakakin ma’aikatar lafiyar yankin Gazan ya bayyana.
Harin ya faru ne a shekaranjiya (Laraba) a lokacin da ake cikin wata yarjejeniyar sa’a hudu ta tsagaita wuta wadda Isra’ila ta kira amma kungiyar gwagwarmayar Hamas ta yi watsi da ita. A wani hari na daban, an bayyana kisan wani sojan Isra’ila a zirin Gazan.
Har ila yau, wasu likitocin Falasdinawa sun ce a wani hari ta sama a lokacin yarjejeniyar, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai a garin Khan Younis.
Gabanin wadannan hare-haren, Isra’ila ta kai farmaki a wata makaranta mallakin Majalisar dinkin Duniya da ke Gaza, inda wasu ’yan gudun hijira Falasdinawa ke neman mafaka.
Fiye da Falasdinawa 1300 da kuma Yahudawa 58 ne suka rasa rayukansu a rikicin zuwa lokacin hada wannan rahoton. Kodayake galibin wadanda suka mutu daga bangaren Falasdinun, fararen hula ne.