Isra’ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza bayan hukuncin Kotun Duniya

Isra’ila ta ce ta tumke ɗamara domin ci gaba da luguden wuta a Gaza.

Isra’ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza bayan hukuncin Kotun Duniya

Akalla Falasɗinawa 174 Isra’ila ta kara kashewa sannan ta raunata 310 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.

’Yan Isra’ila masu kama wuri zauna sun yi kisan kiyashi kan iyalai 18 a Zirin Gaza, inda mutum 174 suka rasu tare da raunata 310 a sa’o’i 24 da suka gabata,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa.

“Akwai mutane da dama da har yanzu sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai da kan tituna yayin da masu aikin ceto suka gaza kaiwa gare su,” in ji sanarwar.

Wannan na zuwa ne dai bayan Kotun Duniya (ICJ) ta kada kuri’ar amincewa da umartar Isra’ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan kiyashi a Gaza.

Alƙalan kotun sun kaɗa ƙuria’a 16 kan cewa akwai bukatar Isra’ila ta dauki dukkan matakan da suka dace na hanawa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa yi wa Falasɗinawa kisan kare dange a Zirin Gaza.

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 3, sun kwato makamai a Taraba
Matashi ya yi yunkurin hallaka kansa kan bashin N2m a Kano

Har ila yau, ta hanyar kuri’a 16, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta ɗauki matakan gaggawa don tabbatar da samar da agajin jin kai da na yau da kullum da ake bukata cikin gaggawa.

A wannan Juma’ar ce dai Kotun Duniyar ta yi zaman karshe na zartas da hukunci kan karar da Afrika ta Kudu ta shigar gabanta.

Ana iya tuna cewa dai, a ranar 29 ga watan Disamban bara ce Afirka ta Kudu ta garzaya gaban Kotun, inda take tuhumar Isra’ila da kisan kare dangi a Gaza.

Wannan dai na zuwa bayan kashe tarin fararen hula da yawansu ya haura dubu 25 galibinsu mata da kananan yara daga ranar 8 ga watan Oktoba kawo yanzu.

Isra’ila dai ta sha musanta zargin bisa kafa hujja da cewa Hamas ta kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 1 da 200 a hare-haren da ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.

Kafin hukuncin, Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce duk inda aka je aka dawo, ba za ta sauya zani ba domin kuwa ɗamara ma yanzu suka tumke ta ci gaba da luguden wuta a Gaza.