Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 40 a Gaza bayan ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya

Sojojin Isra’ila sun kashe Palasdinawa aƙalla 40 a Zirin Gaza, jim kaɗan bayan ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Hamas

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 40 a Gaza bayan ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya

Sojojin Isra’ila sun kashe Palasdinawa aƙalla 40 a sassan Zirin Gaza, jim kaɗan bayan ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Hamas.

Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren a kan gidaje da wasu wurare a Gaza ne a yayin da Falasdinawa a ciki da wajen yankin Gaza suke tsaka da murnar yarjejeniyar zaman lafiyar.

A ranar Laraba ne masu shiga tsakani, Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa — suka tabbatar cewa Hamas da Isra’ila sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar bayan shafe watanni 15 ana gwabza ƙazamin yaki a tsakaninsu.

Masu shiga tsakanin sun bayyana cewa yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi 19 ga watan nan na Janairu, 2024.

Yarjejeniyar za ta kai ga musayar fursunonin da sakin mutanen da kowane ɓangare ke tsare da su, ciki har da Palasdinawa dama da 1,000 da ke hannun Isra’ila.

Ya kuma kunshi janyewar dakarun Isra’ila dafa wasu yankunan Gaza da kuma barin Palasdinawa da suka yi gudun hijira dawowa gidajensu.

Kusoshin adawar Isra’ila, Yair Lapid da Benny Gantz sun bayyana goyon bayansu ga Fira Minista Benjamin Netanyahu da yarjejeniyar zaman lafiyar.