Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 a wata makaranta a Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ba da gan-gan ta kai wannan hari ba.

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 a wata makaranta a Gaza

Jama’a sun ratsa baraguzan makarantar al-Tabin ta garin Gaza biyo bayan wani harin da Isra’ila ta kai a ranar 10 ga watan Agusta wanda ya kashe mutane fiye da 100 [Omar al-Qattaa/AFP]

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 ta kuma jikkata da dama a wani hari da ta kai wata makaranta da ke Daraj a Birnin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran na Falasɗinawa WAFA ya ce tankokin yaƙin Isra’ila sun yi luguden wuta kan makarantar, wacce ta zama mafaka ga Falasɗinawan da suka rasa gidajensu.

“An yi wa fiye da mutum 40 shahada an jikkata da dama bayan harin na Isra’ila a makarantar Al-Taba’een a yankin Al-Sahaba a Birnin Gaza,” kamar yadda mai magana da yawun ’yan sandan yankin Mahmoud Basal ya wallafa tun da farko a saƙon da ya wallafa a Telegram.

Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ba da gan-gan ta kai wannan hari ba, hasali ma ta nufi wani sansanin mayakan Hamas ne, amma kuma harin ya kufce tare da fadawa cikin makarantar Al-Taba’een.

A wata sanarwar ta daban kuma rundunar sojin Isra’ilan ta ce ta sami bayanan sirri da ke nuna cewa mayaƙan Hamas na fakewa cikin fararen hula don samun mafaka a makarantar, shi ya sa ta kai harin kan mai uwa da wabi.

Wannan sabon hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wanda dakarun na Isra’ila suka kai cikin wata makarantar ta daban, inda ya kashe mutane 18, harin da Isra’ila ta ce nan ma kuskure ne.

Isra’ila ta zafafa a hare-hare a Gaza tun bayan kisan shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a kokarin da take yi na ganin cewa mayaƙan na Hamas ba su mayar mata da raddi mai zafi ba.

Sai dai tuni kungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas a ranar Talata ta naɗa Yahya Sinwar a matsayin sabon shugabanta.

Sinwar ya maye gurbin Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a Tehran bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran a ranar 31 ga watan Yuli.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna