Isra’ila ta kashe Falasdinawa 11 ta harbi wasu 80
Falasdinawa 11 sun rasu, wasu 80 sun samu raunukan harbi a wani harin sojojin Isra’ila a Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Falasdinawa 11 sun rasu, wasu 80 sun samu raunukan harbi a wani harin sojojin Isra’ila a Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Hukumar Lafiya ta Falasdinawa ta ce dattawa uku masu shekaru 72, 66 da kuma 61 da wani saurayi dan shekara 16 na daga cikin mutanen da sojojin Isra’ila suka kashe a harin na ranar Laraba a yankin Nablus.
- Samamen DSS a ofishin NNPP ya bar baya da kura
- Sauyin kudi: Muna binciken kalaman tunzurin gwamnoni —Shugaban ’yan sanda
Galibin wadanda sojojin suka kashe ko suka harba fararen hula ne; an kashe Adnan Saabe Baara mai shekara 72 a tsakiyar titi a cikin kasuwa, Anan Shawkat Annab, mai shekara 66 kuma ya rasu ne bayan an garzya da shi asibiti, a cewa Hukumar Lafiya ta Falasdinawa.
Abdul Hadi Ashqar mai shekara 61 da Mohammad Shaaban mai shekara 16 na daga cikin wadanda sojojin Isra’ilan suka harbe har lahira.
Ta kara da cewa harin sojojin Isra’ilar a yankin ya haddasa dauki-ba-dadi tsakaninsu da ’yan sa-kan Falasdinawa, inda aka kwashe sa’a hudu ana ba-ta-kashi.
Rundunar Sojin Isra’ila ta ce ta kashe wasu jagororin mayakan Falasdinawa uku da dakarunta suka ritsa a wani gini, amma suka ki mika wuya.
An kuma kashe wasu mayakan Falasdinawa shida kamar yadda kungiyarsu ta bayyana a kafar sada zumunta ta Telegram.
BBC ta ruwaito cewa Falasdinawa da sojojin Isra’ila suka kashe a harin sun haura na watan Janairu da aka kai yankin Jenin, wanda shi ne mafi muni a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Sama da mutum 80 ne ke asibitoci akalla biyar a yankin inda ake jinyar su bayan harin na ranar Laraba.
Babban jami’in gwamnatin Falasdinawa, Hussein al-Sheikh, ya bayyana harin a matsayin ‘kisan gilla’, shugaban gwamnatin Falasdinawa, Mahmuoud Abbas, kuma ya dora wa Isra’ila laifin tabarbarewar zaman laifya a yankin.
Kungiyar Falasdinawa ta Hamas da ke iko a yankin Gaza ta ce tana “lura da abin da ke faruwa na tashin hankali a Yammacin Gabar Kogin Jordan, kuma abin ya kusa kaiwa makura.”