Isra’ila ta kashe jagoran Hamas a Lebanon
Wannan wata manufa ta janyo Lebanon gadan-gadan cikin yakin Isra’ila da Hamas.
Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugabanta a Lebanon, Saleh al-Arouri, a harin da aka kai a Kudancin birnin Beirut.
An ce al-Arouri na cikin shugabannin ayyukan Hamas na soja.
- Zan daina tallafa wa Gombe United saboda rashin kataɓus — Inuwa Yahaya
- Babu wata ɓaraka a tsakanina da Baffa Bichi — Abba Gida-Gida
Wani babban jami’in tsaro a Beirut ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, an kashe Aruri da wasu masu tsaronsa ne a wani hari da Isra’ila ta kaddamar a yankin unguwar Dahiyeh da ke zama kakkarfar tungar mayakan Hezbollah mai kawance da Hamas.
‘Mutanen da harin ya kashe sun kai shida’
Gidan talabijin na gwamnatin Lebanon ya ce mutanen da suka mutu a harin da ya kashe mataimakin shugaban Hamas a Lebanon sun kai shida.
Tun farko an ba da rahoton cewa mutum huɗu ne suka mutu a harin.
Kungiyar Hamas ta ce an kashe mataimakin shugaban reshenta na siyasa da ke Lebanon Saleh Al-Arouri sakamakon harin da Isra’ila ta kai a Beirut.
Kafafen watsa labaran Lebanon sun ce harin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu mutum biyar.
Hotunan bidiyo sun nuna wata mota na ci da wuta ga kuma wasu gine-gine a kusa sun yi kaca-kaca a unguwar Dahiyah wata sannaniyar matattara ga ’yan Hizbullah.
Saleh Al-Arouri dai na daga cikin kwamandojin da suka kafa rundunar Al-Qassam – wato bangaren soji na kungiyar Hamas kuma an sha daure shi a gida yari a Isra’ila.
An sake shi ne a watan Maris na 2010, a wani bangare na musayar fursononin Falasdinawa don sakin sojan Isra’ilan nan Gilad Shalit.
Tuni Firaministan Lebanon, Najib Mikati ya yi tur da kisan da aka yi wa Aruri, yana mai bayyana harin a matsayin wata manufa ta janyo Lebanon gadan-gadan cikin yakin Isra’ila da Hamas.
Da yammacin wannan Talatar ce aka ji karar wata fashewa a birnin na Beirut, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba a yayin da wasu hotunan da aka watsa ta shafukan sada zumunta ke nuna irin barnar da tashin gobarar ya haifar.
Harin na zuwa ne bayan Kungiyar Agaji ta Red Cross a Falasdinu ta ce, an kashe mutane da dama tare da raunata wasu a wani hari da Isra’ila ta kai shalkwatar birnin Khan Younis da ke Gaza.
Isra’ila ta zafafa kai hare-hare a Lebanon tun bayan afkawar shan mamaki da kungiyar Hamas ta yi ma ta, ranar 7 ga watan Oktobar bara, da ya yi sanadin mutuwar sama da Isra’ila 12,000 da safe sama da 200.
Ko da ya ke an sako wasu daga ciki, ya yin da har yanzu Hamas din ke tsare da Isra’ilawan kamar dai yadda ita ma Isra’ilar ke tsare da dubban Falasdinawa maza da mata da kananan yara.