Isra’ila ta kashe sama da mutane 270 a Lebanon

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana harin na Isra’ila a matsayin ‘rashin hankali’.

Isra’ila ta kashe sama da mutane 270 a Lebanon

Lebanon ta ce, akalla mutane 270 sun rasa rayukansu sakamakon jerin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar a yankin kudancin ƙasar a wannan Litinin.

Kazalika hare-haren na Isra’ila sun jikkata sama da mutane 400 kamar yadda Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Lebanon ta sanar.

Rundunar Sojin Isra’ila ta ce ta kai sama da hare-hare 300 a kan Hezbollah, yayin da ta yi kira ga mazauna kudancin Lebanon ɗin da su fice daga yankin saboda tana shirin ƙaddamar da wasu hare-haren kan mayakan Hezbollah.

Sai dai ita ma ƙungiyar Hezbollah ta ce, ta kai hari kan wasu wurare uku a yankin arewacin Isra’ila.

Adadin mamata fiye da 180, shi ne mafi yawa da aka samu a wani hari da aka kai daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Yakin ya ɓarke ne bayan ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta kai hari mafi muni a kan Isra’ila, yayin da wannan yaƙin ya shafi Hezbollah da sauran ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tuni Iran ta gargaɗi Isra’ila game da abin da ka iya faruwa nan gaba bayan ƙazamin faarmakin da ta kai wa Hezbollah a babban sansaninta da ke Lebanon.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana harin na Isra’ila a matsayin ‘rashin hankali’

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos