Isra’ila ta kashe mutum 500 a asibitin Zirin Gaza

An kai harin ne yayin da Faladinawa suka nemi mafaka a cikin asibitin

Isra’ila ta kashe mutum 500 a asibitin Zirin Gaza

Harin Isra’ila

Akalla mutum 500 ne suka mutu bayan wani hari ta sama da kasar Isra’ila ta kai kan asibitin Al-Ahli Baptist da ke Zirin Gaza a ranar Talata.

Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce asibitin ya cika ba masaka tsinke da marasa lafiya da suke neman mafaka a cikinsa gabanin kaddamar da harin a kan shi.

Asibitoci da dama a Zirin Gaza sun zama mafakar ’yan gudun hijira inda masu zama a cikinsu suke kyautata zaton za su tsira daga hare-haren na Isra’ila.

Tun bayan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba, ita ma Isra’ilan ta mayar da martani inda ta sha alwashin mayar da Zirin Gaza kufai.

Sai dai Kakakin Rundunar Sojin Isra’ila, Riya Admiral Daniel Hagari, ya ce har yanzu babu cikakkun bayanai a kan mace-macen asibitin.

“Za mu samo cikakkun bayanai domin sanar da jama’a; ba zan iya cewa ko wannan harin na Isra’ila ba ne ko kuma a’a,” in ji shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan