Isra’ila ta kawo ƙarshen mamayar da ta yi wa Gaza — Tinubu

Tinubu ya ce dole ne ƙasashen Musulmi su tabbatar an kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Isra’ila ta kawo ƙarshen mamayar da ta yi wa Gaza — Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya yi kira da a kawo ƙarshen tashin hankalin da ke faruwa a Gaza, don rage wahalar da miliyoyin al’umma ke fuskanta sakamakon rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

Da yake magana a wani taron ƙasashen Larabawa da Musulmai a Birnin Riyadh na Ƙasar Saudiyya, Tinubu ya bayyana goyon bayan Najeriya na nemar wa Isra’ilawa da Falasɗinawa damar rayuwa tare cikin lumana.

Ya ce, “Rikicin a Falasɗinu ya daɗe ana yinsa, yana jefa rayuka cikin wahala mai tsanani.

“Muna da nauyin da ke kanmu na kawo ƙarshen wannan rikici – ba wai mu tsaya wajen yin suka kawai ba.”

Tinubu ya jaddada buƙatar girmama haƙƙoƙin fararen hula, inda ya nemi a samu daidaito a rikicin Gabas ta Tsakiya.

Ya ce, “A tsarin duniya da ke bisa doka, kowace ƙasa na da haƙƙin kare kanta, amma ya zama dole a yi la’akari da daidaito.

“Ba za a iya ɗaukar rayuwar duk wata al’umma da burinsu na gaba a matsayin abin da ba shi da muhimmanci ba.”

Ya yaba wa shugabannin Saudiyya kan shirya taron, inda ya tabbatar da cewa Najeriya za ta tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tinubu kuma ya bayar da shawara kan kafa wani ofishi da zai ke duba da kuma ya bayar da rahoto game da aiwatar da ƙudurorin taron, da fatan kawo zaman lafiya mai ɗorewa.