Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza
Bisa ƙa’ida dai ya kamata yarjejeniyar ta fara aiki da misalin ƙarfe 7:30 agogon GMT.
A safiyar wannan Lahadin ake sa ran yarjejeniyar tsagaita wuta za ta soma aiki a yaƙin da ake fafatawa tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas a Gaza.
Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ministocin Isra’ila ta kaɗa kuri’ar amincewa da yarjejeniyar sulhu da kuma sakin fursunonin da ke hannun ɓangarorin biyu.
Bisa ƙa’ida dai ya kamata yarjejeniyar ta fara aiki da misalin ƙarfe 7:30 agogon GMT.
Sai dai kuma wata sanarwa da mai magana da yawun sojin Israila, Daniel Hagari ya fitar safiyar wannan Lahadin, ya ce Isra’ila ba za ta aiwatar da tsagaita wuta ba har sai Hamas ta fitar da jerin sunayen ragowar Isra’ilawan da take riƙe da su.
Wannan sabon sharaɗin da Isra’ilar ta bai wa Hamas da alama na neman kawo tsaiko dangane da yarjejeniyar, inda yanzu haka rahotanni ke nuna cewa tuni dakarun Isra’ilar sun ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a yankin na Gaza.
Sabbin hare-haren Isra’ila ta ƙaddamar safiyar yau sun yi sanadiyyar kashe mutum takwas kamar yadda mai magana da yawun hukumar sojin sa-kai ta Gaza da ke ƙarƙashin Hamas ya bayyana.
An kashe mutum biyar a Gaza kamar yadda Mahmoud ya ce sannan mutum uku kuma a arewacin ƙasar, inda mutum 25 kuma suka samu raunuka.
Wani bidiyo daga Rafah da ke kudancin Gaza ya nuna yadda mutane tuni suka fara barin gidajensu, amma dakarun Isra’ila sun yi gargaɗin cewa kada fararen hula su kusanci yankunan da ta kange ko kuma gine-ginensu ko ma’aikatanta.