Isra’ila ta soma saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon
Rahotanni na cewa sojojin Isra’ila sun soma saɓa ƙa’idar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakaninta da Lebanon. Kawo yanzu sojojin sun saɓa yarjejeniyar sau bakwai, ciki har da harbi a ƙauyukan da ke kudancin Lebanon, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Lebanon NNA ya bayyana. Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe Van […]
Rahotanni na cewa sojojin Isra’ila sun soma saɓa ƙa’idar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakaninta da Lebanon.
Kawo yanzu sojojin sun saɓa yarjejeniyar sau bakwai, ciki har da harbi a ƙauyukan da ke kudancin Lebanon, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Lebanon NNA ya bayyana.
- Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe
- Van Nistelrooy da Lampard sun samu aikin horaswa a Ingila
An ba da rahoton cewa saɓa yarjejeniyar ta fi faruwa ne a gundumar Marjayoun ƙarƙashin yankin Nabatieh da kuma gundumar Tyre.
Wata tankar yaƙin Isra’ila ta harba bam wani gida a yankin Tel Nahas kusa da Burj Al-Moulouk, inda mai gidan ya tsallake rijiya da baya, wanda bai jima da shiga gida ba, a cewar NNA.
Sojojin sun kuma harba bama-bamai garuruwan Markaba da Talloussa da Odaisseh da Taybeh da kuma Houla, sannan sun tura tankokin yaƙi huɗu zuwa yammacin Khiyam.
A Khiyam, an ba da rahoton cewa sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan wasu mutane da suke tafiya wajen jana’iza.
Haka kuma a wani wajen, motocin rushe gini na Isra’ila sun tunɓuke bishiyoyin zaitun sun kuma share gonaki a yankin Abbara da ke Kfarkela.
Sai dai a martanin da Isra’ila ta yi kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito, ta ce ta yi harbe-harbe a Kudancin Lebanon akan mutanen da suka saɓa yarjejeniyar tsagaita wutar da ta yi da Hezbollah.
Tuni dai Shugaban Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bai wa dakarun umarnin zama cikin shirin buɗe wuta da zarar an saɓa yarjejeniyar da suka ƙulla.
A ranar Laraba ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah da Amurka ta shiga tsakani ta fara aiki da ƙarfe 4 na safiya da, matakin da tuni Iran ta yi maraba da shi.
Yarjejeniyar za ta sa Isra’ila ta daina yaƙin da take yi a Lebanon wanda ya kashe aƙalla mutum 4,000, da jikkata fiye da mutum 16,000 kana ya tilasta wa fiye da mutum miliyan ɗaya barin gidajensu.
Yarjejeniyar dai ta soma aiki awanni bayan Isra’ila ta ƙaddamar da mummunan luguden wuta ta sama a babban birnin ƙasar wato Beiruta wadda ke zuwa yayin da al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya, waɗanda ke cikin mawuyacin hali, suke ɗari-ɗari game da ɗorewarta.
Mazauna Beirut sun riƙa bukukuwa na murnar aiwatar da wannan yarjejeniya kuma babu wasu rahotanni na ƙin yin biyayya ga yarjejeniyar tun da aka tsagaita wuta.
Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda aka sanar da ita ranar Talata wani babban ci gaba ne wajen kawo ƙarshen yaƙin kusan watanni 14 da aka fafata baya ga ta’azzara yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza.
A ɓangare guda, mayaƙan Hezbollah sun kashe sojojin Isra’ila aƙalla 82 da fararen-hula 47, a cewar hukumomi.
Isra’ila ta ce za ta kai hare-hare muddun ƙungiyar Hezbollah ta karya yarjejeniyar. Kawo yanzu Hezbollah ba ta ce komai ba game da lamarin.
Me yarjejeniyar ta ƙunsa?
A yammacin Talata ne Isra’ila da Faransa da Amurka suka sanar da ita, inda Shugaba Joe Biden ya ce ana fatan “za ta zama ta dindindin.”
Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa manema labarai cewa an tsara yarjejeniyar ce “da zimmar ta zama ta dindindin”.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, cikin kwana 60 Hezbollah za ta janye dakarunta da makamai daga yankin da ake kira Blue Line — wata iyaka da ba ta hukuma ba tsakanin Isra’ila da Lebanon wadda aka ƙirƙira a ƙarshen yaƙin da suka gwabza a 2006 — da kuma kogin Litani da ke da nisan kilomita 30.
Dakarun sojin gwamnatin Lebanon za su maye gurbin mayaƙan Hezbollah a yankin, sannan su tabbatar babu wasu sauran makamai ko kayayyakin ƙungiyar da za a sake ginawa, a cewar wani babban jami’in Amurka.
Cikin wannan kwana 60 ɗin dai, Isra’ila za ta dinga janye dakaru da fararen hularta da suka rage, in ji Biden, yana mai cewa hakan zai bai wa fararen hula a ɓangarorin biyu damar komawa gidajensu.
“Wannan sanarwar za ta shimfiɗa ƙa’idojin samun zaman lafiya da zai bai wa ƴan ƙasashen biyu damar komawa gidajensu,” in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da ta fito daga gwamnatocin Amurka da Faransa, ƙasashe biyu da za su taimaka wurin tabbatar da tsare-tsaren da ke ƙasa wanda za su aiwatar da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar a ƙarshen yakin shekarar 2006.
Firaministan Lebanon, Najib Mikati ya yi maraba da yarjejeniyar, yana mai cewa wani muhimmin mataki ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tare da bai wa ƴan ƙasar damar komawa gida.
Sai dai kuma ya buƙaci Isra’ila ta “bi ƙa’idojin yarjejeniyar” ta fice daga yankunan da ta mamaye da kuma mutunta ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Shi kuwa Ministan Muhalli na ƙasar Labanon Nasser Yassin, ya shaida wa BBC cewa, ganin yadda ƙungiyar Hezbollah ta ci gaba da kasancewa a matsayin “jami’yya” a majalisar dokokin ƙasar, a yanzu ƙasarsa na buƙatar mayar da hankali kan maido da tsarin siyasa da sawwaƙa tattaunawa tsakanin “al’ummomi daban-daban”.